Kungiyar Real Madrid ta mika Naira Biliyan 80 domin ta dauke Mbappe daga PSG

Kungiyar Real Madrid ta mika Naira Biliyan 80 domin ta dauke Mbappe daga PSG

  • Kylian Mbappe ya ki sabunta kwantiraginsa da Paris Saint-Germain
  • Real Madrid tana neman a saida mata ‘dan wasan a kan miliyan $188
  • Idan ciniki ya fada, ‘Dan wasan gaban zai bar Lionel Messi da Neymar

Mbappe yana neman barin PSG ne?

Paris - A karshen kakar shekarar banan ne wa’adin ‘dan wasan gaban kasar Faransa, Kylian Mbappe zai kare a kungiyar Paris Saint-Germain.

Rahotanni daga Goal.com sun bayyana cewa sau shida Paris Saint-Germain tana neman ‘dan wasan ya sabunta kwantiraginsa, amma ya ki yarda.

Tuni Real Madrid ta bukaci PSG ta saida mata ‘dan wasan, ta kuma gabatar da fam miliyan €160 (£137m/$188m) domin a sallama mata tauraron.

A lissafin kudin mu na gida, wannan zunzurutun kudi ya tashi a kan kusan Naira biliyan 80 kenan.

Da gaske Real Madrid ta ke yi

Kara karanta wannan

‘Yan kwangilar China sun sa lokacin da za a gama aikin jirgin kasan da zai hada Kano da Kaduna

Rahoton ya nuna kungiyar ta Madrid tana sa ran ta iya dauke Kylian Mbappe mai shekara 21 kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasan shekarar nan.

Duk da cewa Real Madrid tana fama da karancin kudin-shiga a dalilin annobar COVID-19, ta dage a kan dauko daya daga cikin taurarin da ake ji da su.

Mbappe a PSG
Kylian Mbappe Hoto: www.football-espana.net
Asali: UGC

A ina aka tsaya a cinikin?

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez da kansa ya shiga cikin wannan ciniki. Yanzu haka kungiyoyin na cigaba da tattunawarsu a asirce.

Akwai kyakkyawar alaka tsakanin Florentino Perez da shugaban kungiyar PSG, Nasir El-Khelafi, sannan Mbappe yana sha’awar buga wa Real Madrid.

Yanzu inda matsalar ta ke shi ne kungiyoyin biyu su amince da farashin da za a saida ‘dan wasan domin ba zai yi wahalar amince wa da koma wa Sifen ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin Shugaban Majalisa da karbar cin hancin Naira Biliyan 4 domin ya canza zubin PIB

Da aka tambayi Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti a game da ‘dan wasan, yace bai san ko za a kawo masa shi ba, amma yace yana da ‘yan kwallonsa.

Ronaldo zai koma Faris kenan?

A baya kun ji cewa Kungiyar PSG tana kokarin dauko Cristiano Ronaldo daga Juventus, ya buga kwallo tare da Lionel Messi, Neymar Jr., da su Sergio Ramos.

Ganin Kylian Mbappé ya dage sai ya bar Paris Saint-Germain ya sa PSG ta ke tunanin dauko Ronaldo daga kasar Italiya idan har ta rasa matashin 'dan wasan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng