Za a Fafata Tsakanin Sanatoci Wajen Neman Kujerun Shugabancin Majalisar Dattawa

Za a Fafata Tsakanin Sanatoci Wajen Neman Kujerun Shugabancin Majalisar Dattawa

  • An zabi shugabannin majalisar tarayya, yanzu akwai ragowar manyan kujeru shida da su ka rage
  • Za a tsaida shugaban masu rinjaye, marasa rinjaye, shugaban masu tsawatarwa da mataimakansu
  • Shugabancin bangarorin masu rinjaye da marasa rinjaye ya raba kan Sanatoci a Majalisar Dattawa

Abuja - A yayin da majalisar dattawa ta ke shirin yin zama a ranar Talata, hankali duk ya karkata ga wadanda za su samu shugabancin bangarori.

Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa Michael Opeyemi Bamidele Bamidele (APC, Ekiti) daAminu Waziri Tambuwal (PDP, Sokoto) su na kan gaba a takarar.

A makon nan za a zabi shugaban masu rinjaye da shugaban marasa rinjaye. Haka zalika za a zabi sauran shugabanni shida da ake da su a majalisar.

Majalisar Dattawa
Sanatoci a Majalisar Dattawa Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Sai dai Sanata Muhammad Ali Ndume (APC, Borno) da Sanata Muhammad Adamu Aliero (PDP, Kebbi) za su gwabza da Bamidele da Tambuwal.

Kara karanta wannan

Ana So a Kunno Sabon Wuta: An Bukaci Tinubu Ya Ajiye Wike Sannan Ya Nada Wani Shaharren Dan Siyasar Ribas Mukamin Minista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume/Bamidele a APC

Ali Ndume da mataimakinsa a kwamitin yakin neman zaben Akpabio/Barau, Sanata Bamidele su na harin kujerar shugaban masu rinjaye daga APC.

Ndume ya taka rawar gani a zaben Akpabio kuma ya taba rike wannan kujera, sai dai Sanatan na Ekiti ya fito daga yankin da ya dace a kai kujerar.

A bangaren marasa rinjaye, wasu shugabannin jam’iyyar PDP su na goyon bayan tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal ya kare hakkinsu.

Rikicin da yake PDP

Sai dai Nyesom Wike da mutanensa su na yakar Tambuwal kamar yadda su ka sha bambam da jagororin jam’iyyar a zaben majalisar wakilan tarayya.

Jaridar ta ce tsohon Gwamna kuma Sanatan Kebbi ta tsakiya a majalisar dattawa, Muhammad Adamu Aliero ya nuna ya na sha’awar wannan kujera.

Aliero ya na kan wa’adinsa na hudu kenan a majalisa, ya lashe zabe a 2007, 2015, 2019 da 2023.

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Goyi Baya Ba": Kungiyar PDP Ta Ki Amincewa Da Zabin Tambuwal A Matsayin Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisa, Ta Bada Dalili

A wani rahoton na dabam, wasu ‘yan adawa su na goyon bayan Sanatan Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi, bisa dukkan alamu za a fafata a zaben na gobe.

Wasu sun fara korafi

A kwanakin baya aka ji labari kujerar shugaban marasa rinjaye ta na neman haddasa rigima tsakanin Sanatocin jam'iyyun adawa a Majalisar Dattawa.

Aminu Tambuwal, Abdulrahman Sumaila Kawu da Abba Moro sun fitar da takarda, su na kukan cewa APC na neman tsoma masu baki kan harkarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel