Tinubu Zai Fuskanci Barazana, Lauyoyi 8 Za Su Kai Shi Kotu Kan Harajin Abin Hawa

Tinubu Zai Fuskanci Barazana, Lauyoyi 8 Za Su Kai Shi Kotu Kan Harajin Abin Hawa

  • Kungiyar NBA ba ta gamsu da harajin POC da masu abin hawa za su fara biya a shekarar nan ba
  • ‘Yan NBA-SPIDEL sun nuna sai inda karfinsu ya kare a kotu domin ja da gwamnatin Bola Tinubu
  • Lauyoyin za su ji ko ana da damar tilasta biyan N1000 domin samun takardar mallakar abin hawa

Abuja - Wani sashe na kungiyar NBA ta lauyoyin Najeriya zai yi shari’a da gwamnatin tarayya a dalilin wani sabon haraji da aka fito da shi.

A ranar Litinin, Vanguard ta fitar da rahoto cewa ‘yan kungiyar NBA-SPIDEL masu kare jama’a, sun kafa wani kwamiti da zai duba batun harajin POC.

Za a bukaci duk wani mai abin hawa ya biya harajin N1000 a kowace shekara domin ya samu takardar mallaka, wasu na da ta-cewa a game da harajin.

Kara karanta wannan

Tsofaffin Janarori Sun Jero Shawarwarin Kawo Karshen Matsalolin Tsaro

Tinubu
Shugaban kasa, Bola Tinubu a Legas Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Ganin za a rika sabunta biyan wannan kudi duk shekara domin mai abin hawa ya tabbatar da mallaka, lauyoyi su ka ga bukatar a garzaya kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matsayar NBA-SPIDEL kan POC

Shugaban NBA-SPIDEL da sakatarensa na kasa, John Aikpokpo-Martins da Funmi Adeogun sun fitar da sanarwa da ta nuna za su yi kara a kotu.

Lauyoyin sun nuna za su tashi tsaye domin kare taalaka daga dokokin zalunci da duk wasu tsare-tsraen gwamnati da ake tunanin sun saba doka.

Aikpokpo-Martins da Adeogun su ka ce shari’ar da su yi da gwamnatin tarayya ta na cikin nauyin da yake kan NBA na ba duk mara karfi kariya.

Rahoton ya ce kungiyar ta kafa kwamitin da za tayi amfani da hanyar da doka ta halatta domin kalubalantar wannan haraji da ake shirin kakabawa.

Kafin a bukaci masu abin hawa su fara biyan wannan kudi a duk shekara, kungiyar lauyoyin ta ce za ta garzaya zuwa kotu ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

An tanadi Lauyoyi na musamman

Kamar yadda Nairaland ta kawo rahoto, Lauyoyin da za su tsayawa NBA-SPIDEL sun hada da Kunle Edun, Francis Ogunbowale da Maxwell Opara.

Ragowar lauyoyin su ne Felix Akpowowo, Adeola Folarin, Ibrahim Al-Hussein da Izu Aniagu sai Ikeazor Akaraiwe, SAN a matsayin mai bada shawara.

Gwamnati za ta tara N12bn

Dazu labari ya zo cewa harajin POC da za a fara biya a shekarar nan zai jawo gwamnatin tarayya ta samu kusan Naira biliyan 12 a asusunta.

Idan mafi yawan masu motoci, gingimari, babura da keke napep su ka yi biyayya ga dokar, za a samu Biliyoyi a lokacin da ake kuka kan kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel