Jihar Zamfara
Bama bamai sun tashi a jihar Zamfara. Wannan ne karo na 3 da bam ke tashi a jihar. Ana zargin yan ta'adda sun dasa su a kan titunna 3 a jihar a cikin makon guda.
Kungiyar gwamnoni ta Najeriya NGF ta nuna damuwa kan harin bam da ake zargin ƴan ta'adda da dasawa a titin Dansadau a jihar Zamfara, ta yi alhini.
Rundunar sojin saman Najeriya ta kai hari kan sansanin 'yan ta'adda a Rugan Mai Taru, jihar zamfara, inda ta hallaka 'yan ta'adda da dama tare da lalata sansanin su.
Yan ta'adda sun dasa bama-bamai a garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a Zamfara inda yan sanda suka zargi kungiyar Lakurawa da alhakin kai harin.
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta zargi sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Lakurawa da alhaki wajen dasa bama-bamai a wasu kauyukan jihar.
Mutane 12 sun mutu a Yar Tasha, Zamfara, bayan motar haya ta taka wani abin fashewa. An nemi gwamnati ta dauki mataki don dakatar da wannan barazanar.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa an yi arangama tsakanin yan bindiga kan neman iko tun bayan mutuwar Halilu Sububu inda aka kashe wani kwamanda.
Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ƴan kwadago, za a fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a watan Maris, 2025.
Ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Gusau na neman albashin wata shida, alawus, da karin girma ko shiga yajin aiki. Suna zargin ba a gyara albashinsu ba.
Jihar Zamfara
Samu kari