Albashin ma'aikata
Bayanai sun nuna ‘Yan majalisar Najeriya za su tashi da kusan Naira biliyan 50 daga cikin baitul-mali a shekarar 2024 a matsayin albashi da alawus.
Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya ta gabatar da taron kwamitin da aka kafa yau Laraba.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana kan nazarin yiwuwar fara amfani da wani sabon tsarin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati na 'iya kokarinka, iya albashinka.'
Kudirin karin albashi ga shugaban alkalan Najeriya da sauran ma'aikatan shari'a ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa a yau Alhamis 9 ga watan Mayu.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce gwamnonin Najeriya suna kaunar ganin ma'aikata cikin walwala kuma a shirye suke su biya sabon mafi ƙarancin albashi.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ba da umarnin fitar da Naira biliyan 5 domin biyan kudaden 'yan fansho a jihar. Wannan dai shi ne karo na 2 a wata 6.
Gwamnatin jihar Kano ta ce ba gaskiya ba ne cewa za ta kori masu sharar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka aiki kamar yadda wasu ke yadawa.
Kungiyar masana harkokin ma'aikatan Najeriya (NECA) ta gargadi gwamnatin tarayya kan jinkirin karin albashi ga ma'aikata. Ta ce jinkirin na kawo cece-kuce.
Ana rade-radin cewa gwamnatin tarayya ta yi wa Sanatoci da 'Yan majalisa karin albashi. Mun tattaro martanin jama’a yayin da aka ji an kara albashin majalisa a boye
Albashin ma'aikata
Samu kari