Siyasar Najeriya
Kotun koli ta Najeriya ta bayyana zaben ciyamomi da aka gudanar a jihar Rivers ranar 5 ga watan Oktoba, 2025 ya saɓawa tanadin doka, don haka bai inganta ba.
Tsohon dan takarar gwamna a jihar Anambra da ya sauya sheka zuwa APC ya ce yana fatan Peter Obi ya biyo shi zuwa jam'iyyar APC domin kawo cigaba a Najeriya.
Shugaban hukumar EFCC, Olanipekun Olukoyede ya yi tone-tone kan yadda ya kaucewa yunkurin wasu yan siyasa da ke neman ba shi cin hanci yayin jana'izar mahaifiyarsa.
Rikicin da ke gudana a majalisar jihar Legas ya dauki sabon salo bayan an janye dukkanin jami’an tsaron da ke gadin shugabar majalisar, Mojisola Meranda.
Jam'iyyar APC ta amince yankin Arewa maso Yamma ya ci gaba da shugabancin jam'iyya mai mulki, hakan ya ƙara tabbatar da Abdullahi Ganduje a kujerarsa.
Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce kwamitin gudanarwa karƙashin jagorancinsa ya gaji bashin kudi Naira biliyan 8.9 da ya karbi jagoranci.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya yi martani ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i na cewa akwai baraka a cikin jam'iyyar APC, inda ya ce kansu a hade yake.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya bayyaka cewa ya kamata Arewa ta mutunta tsarin karɓa-karɓa a zaben shugaban ƙasar da ke tafe a 2027.
Sakataren APC na kasa ya ce ba gaskiya kan cewa Bola Tinubu zai sauke Ganduje daga shugabancin APC yayin da za a yi taron NEC a Abuja ranar Laraba.
Siyasar Najeriya
Samu kari