Siyasar Najeriya
Kungiyar matasan Arewa ta TNYF a jihohi 19 da Abuja ta fitar da tsarin samawa Tinubu kuri'u miliyan 5.5 a 2027 a Arewa yayin ziyara ofishin Sanata Barau Jibrin.
Sanatocin Kebbi guda uku, Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu) sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Jam'iyyar APC ta jihar Kebbi ta kama hanyar faɗawa rikici yayin da ake shirye-shiryen karaɓar sanatocin PDP uku, an dakatar da shugabanni da kusoshi a yankin Koko.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa zargin da ake masa na juyawa Bola Tinubu baya ba gaskiya ba ne, ya ce an masa gurguwar fahimta.
Shugabannin jam'iyyar SDP sun karbi mutane sama da 2,000 da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC da PDP. Shugaban SPD ya ce suna fatan nasara a 2027.
Tsohon mai magana da yawun PDP, Kola Ologbondiyan ya yi ikirarin cewa gwamnoni da sauran ƴan siyasar da ke komawa APC mafutarsu kawai suke dubawa.
Wike ya nemi PDP ta kai tikitin 2027 Kudu. Ya ce ware tikitin 2023 zuwa Arewa ya haifar da rikici amma ana ganin Wike na kokarin hana Atiku takara a jam'iyyar ne.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa son rai ka iya karisa murkushe PDP tun kafin zaɓen 2027, yana mai cewa jam'iyyar ba za ta kai labari ba.
Saraki zai jagoranci kwamitin dinke barakar PDP. An ce kwamitin zai tabbatar da cewa an yi taron NEC da babban taron jam'iyyar cikin nasara don tunkarar 2027.
Siyasar Najeriya
Samu kari