Siyasar Kano
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC ta bayyana dan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan a matsayin wanda ya lashe zaben Shanono da Bagwai.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci mazauna kananan hukumomin Shanono, Bagwai, Ghari da Tsanyawa su zabi yan takarar NNPP a zaben cike gurbi ranar Asabar.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya tayar da kura saboda yawan jama'a a taron kamfen APC na zaben cike gurbin da za a yi a Kano.
Yayin da ake tunkarar zaben 2027 a jihar Kano, ana ta hasashen cewa akwai rarrabuwar kai cikin APC inda magoya baya suka kasu tsakanin jiga-jiganta.
Wani jigon APC, Kwamred Faizu Alfindiki ya yi magana kan siyasar jihar Kano inda ya shawarci Sanata Rabiu Kwankwaso ya nemi afuwar Abdullahi Umar Ganduje.
Wasu tsofaffin mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa NNPP a jihar Kano. Sun dai fito ne daga mazabar tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin Kano ta soke kwangilar titin Jaba-Gayawa bayan bidiyon Dan Bello da ya nuna yadda titin ya lalace. An kuma amince a kashe N14.8bn kan manyan ayyuka.
Shugaban majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce zai yi takarar gwamnan Kano karkashin jam'iyyar ADC. Ya yi magana kan hadakar yan adawa a 2027.
Rahoton kwamitin bincike da aka kafa a Kano ya gano abubuwa da dama game da laifin da ake zargin tsohon kwamishinan sufuri, Ibrahim Ali Namadi da aikatawa.
Siyasar Kano
Samu kari