Jam'iyyar PDP
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce ba zai iya goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ba saboda ba ya mutunta yarjejeniya.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki jam'iyyarsa ta PDP. Wike ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta shirya ba don tunkarar zaben 2027.
Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa ba zai goyo bsyan Atiku Abubakar ba a 2027 kamar yadda ya yi a zaɓen 2023, ya ce sai 2031 ɗan Arewa zai karbi mulki.
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa ko kaɗan bai ci amanar PDP don bayyana shirinsa na marawa shugaban kasa, Bola Tinubu baya a 2027.
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai yafe wa gwamna Fubara ne kawai idan ya nemi gafara da gaskiya yayin da suke rikicin siyasa.
Hajiya Ummu Gada ta koma APC tare da wasu mambobin PDP a Sokoto, tana zargin PDP da rashin adalci da kuma yaba wa ayyukan Gwamna Ahmed Aliyu a jihar.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce bai kamata birnin tarayya Abuja ya kasance a hannun 'yan adawa ba. Ganduje ya ce APC za ta kwace Abuja a 2027.
Jam'iyyar PDP a Abuja ta fara sayar da fom ga masu sha'awar tsayawa takara, inda ciyaman zai biya N8.5m, kansila N1.5m, mma mata za su samu fom din kyauta.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya nuna goyon bayansa ga tazarcen gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno a 2027. Ya ce suna tare da shi.
Jam'iyyar PDP
Samu kari