Jihar Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya gwangwaje wata Hajiya da kyautar kudade. Gwamna Mutfwang ya ba ta kyautar ne kan mayar da kudaden da ta tsinta a Saudiyya.
An shafe kusan watanni uku kenan da nada sabon shugaban APC, Nentawe Yilwatda amma har yanzu bai yi murabus daga mukamin minista ba a ma'aikatar jin kai da walwala.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan makiyaya a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka wani makiyayi tare da kashe shanu masu yawa da sace wasu.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya kwararo yabo ga uwargidan shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu. Ya ce tana nunawa jihar Plateau kauna sosai.
Atiku Abubakar ya soki Shugaba Bola Tinubu kan ziyararsa zuwa jihar Filato, yana cewa shugaban ya fi son shagali da manyan jam’iyyarsa fiye da tausaya wa jama’a.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce burinsa shi ne haɗa kan al’ummar Najeriya, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta yi adalci ga dukkan addinai.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shi mutun ne da yake mutunci addinin da kowa ya zabi bi, inda ya ce bai taba kokarin musuluntar da matarsa ba.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar su guji bambancin addini da kabilanci, yana mai cewa ƙauna da zaman tare su ne ginshiƙan ci gaba.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai halarci jana'izar shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwada a Filato. Zai gana da shugabannin Kiristocin Arewa a Jos.
Jihar Plateau
Samu kari