Labaran NNPC
Yayin da ake cigaba da rigima kan farashin man fetur tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Aliko Dangote, Gwamnatin Tarayya ta fadi matsayarta kan haka.
Rabaran Gabriel Abegunrin ya ba gwamnatin tarayya shawara kan yadda fetur zai yi arha. malamin addinin ya bukaci a bar Dangote ya sayar da fetur ga 'yan kasuwa.
Kungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas na kasa (PENGASSAN) ta ce za a samu matsala idan yan kasuwa su ka fara sayo fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta IPMAN ta ce sun fara tattaunawa da matatar Ɗangote domin fara ciniki kai tsaye ba tare da biyowa ta hannun NNPCL ba.
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana yakinin cewa za ta iya fara sayen fetur kai tsaye daga matatar Dangote yayin da tsadar fetur ke kamari.
Tsohon shugaban NESG, Kyari Bukar ya bayyana cewa Bola Tinubu ya biyo hanya mai gargada wajen tuge tallafin man fetue shiyasa aka shiga ƙangin wahala.
Matatar Dangote ta musa kamfanin NNPCL kan adadin man fetur da ta tace. NNPCL ya ce ya loda lita miliyan 16.8 amma matatar Dangote ta ce lita miliyan 111 ne.
Kamfanin mai na NNPCL ya ce nan da karshen shekara matatar man fetur ta gwanatin tarayya a Fatakwal za ta dawo aiki. NNPCL ya bukaci yan jarida su masa adalci.
Kungiyar yan kasuwar man fetur sun ce har yanzu ba su samu man fetur da aka tace daga matatar Dangote ba saboda rashin daidaito kan farashin fetur da NNPCL.
Labaran NNPC
Samu kari