Matasan Najeriya
Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruq Lawal, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24. Ya kuma haramta duk wata zanga-zanga a fadin jihar domin kare rayuka.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnoni hudu sun sanya dokar hana fita ta awanni 24 a jihohinsu yayin da zanga zangar lumana ta rikide zuwa tashin hankali.
Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta yi magana kan harin da aka ce an kaiwa ofishinta na Nyanya a ranar Alhamis bayan da aka fara zanga-zanga.
Rundunar 'yan sanda ta yi shirin ko ta kwana yayin da masu zanga-zanga suka kashe jami'in dan sanda 1 da kuma lalata ofisoshin rundunar a sassan kasar.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun bankado wani sanata da ke daukar nauyin zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wasu matasa guda hudu da ke aiki a wani gidan mai a jihar Borno yayin da zanga-zangar yunwa ta rikide zuwa tashin hankali.
Rundunar 'yan sanda a jihar Niger ta tabbatar da kama wasu mutane 11 da ake zargi da hannu a saka wutar a sakatariyar karamar hukumar Tafa a jihar.
Wasu fusatattun matasa sun kona hedikwatar jam'iyyar APC yayin da suka wawushe kayan da ke ciki. An ce masu zanga-zangar sun kuma lalata kadarorin jihar Jigawa.
Gwamnatin Kaduna ta ce babu wata dokar hana fita da aka sanya a jihar. Uba Sani ya ce yanzu an dawo da kwanciyar hankali a jihar bayan ta'addancin masu zanga-zanga.
Matasan Najeriya
Samu kari