Hukumar yan sandan NAjeriya
Gwamnatin Kano ta karrama dan bangar da aka kashe yana aiki tare da ba matarsa da yayaensa makudan kudi, ta kara girma ga wanda ya samu raunuka yayin aiki.
Nasarorin da rundunar 'yan sandan Kano ke bayyanawa, musamman ta fuskar cafke barayin lokacin zanga-zanga ya jawo barazanar kawo karshen rayuwar kakakin rundunar.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci jami'an tsaron Najeriya da su kawo karshen masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da ke a fadin kasar nan.
Wani jirgin ruwa da ya dauko kayayyaki da fasinjoji ya gamu da hatsari a jihar Bayelsa. Jirgin ya gamu da hatsarin ne yana kan hanyar zuwa birnin Yenagoa.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty International ta caccaki hukumomin Najeriya bisa samamen da su ka kai ofishin kungiyar kwadago ta kasa.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta fusata kan samamen da jami'an tsaro suka kai a hedkwatarta da ke birnin tarayya Abuja. Ta ce hakan abin kunya ne.
An samu bambancin furuci tsakanin hukumomin tsaron kasar nan a kan harba bindiga yayin zanga-zangar lumana da matasan kasar nan ke gudanarwa saboda tsadar rayuwa.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Bauchi ta tabbatar da kisan wani matashi Habibu a lokacin da matasa suka yi arangama da sojojin Operation Safe Haven a Lere.
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da kama wasu ‘yan kasashen waje da ke daukar nauyin masu zanga-zanga suna daga tutar kasar Rasha a Kano. Bayanai sun fito.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari