Manyan Labarai A Yau
Matatar mai ta Dangote ta ba hakikance cewa za ta fara samar da man fetur a cikin watan Agusta. Matatar ta sha sanya lokacin fara fitar da man fetur tana dagewa.
Jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ta nuna goyon bayanta ga Gwamna Siminalayi Fubara na jihar. Jam'iyyar karkashin jagorancin Emeka Beke ta ce lokacin siyasa ya kare.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Salman Garba Dogo, ya bukaci jami'an 'yan sandan da aka yiwa karin girma su jajirce wajen kawar da laifuka a jihar.
Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fito ya caccaki manufofin da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kawo a kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta shawarci masu son a canza gwamnati a kasar nan da su jira har sai lokacin zaben 2027. Dele Alake ne ya ba da wannan shawarar.
Kungiyar kafafen yada labaran Arewa (NBMOA) ta shigar da kara kan tashar talabijin ta Arewa24 gaban hukumomi bisa zargin bata al'adun al'ummar Hausawa.
Matatun man fetur suna da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Akwai matatun mai guda 825 da ke aiki. Ga jerin guda 10 da suka fi girma.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi. 'Yan bindigan sun hallaka wani babban basarake yayin harin.
Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin dalibai, Asefon Sunday, ya bukaci matasan Najeriya da su kara hakuri da wannan gwamnati mai ci.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari