Manyan Labarai A Yau
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ya gargadi masu aikata laifuka a jihar Kano da su shiga taitayinsu ko su fuskanci fushin hukuma
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bukaci 'yan siyasan Sokoto da su yi koyi da takwarorinsu na jihar Kebbi wajen hadin kai a tsakaninsu.
Kungiyar gwamnonin PDP ta aika da sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Kungiyar ta bukaci Tinubu ya sake duba manufofin gwamnatinsa kan tattalin arziki.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya daga kasar Brazil bayan ya halarci taron kasashen G20. Tinubu ya kuma yi wasu tarurruka a.ƙasar.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da sabon mafi karancin albashi gama'aikatan jihar. Gwamnan ya amince a fara biyan sabon albashin daga watan Disamba.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi wa 'yan sandan jihar Kano sha tara ta arziki. Barau ya ba su babura domin inganta ayyukansu.
An samu tashin gobara a asibitin koyarwa na jam'iar LAUYECH da ke jihar Oyo. Gobarar wacce ta tashi a asibitin ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin naira.
Wasu fusatattun mutane sun bankawa wasu masu karbar kudaden haraji wuta a ajihar Anambra. Mutanen sun dauki matakin ne bayan an rasa ran wani mutum.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta ci gaba da aikin da take yi na kai samame kan shagunan caca a jihar. Hisbah ta ce ba za ta sassauta ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari