Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kogi ta nuna takaicinta kan harin da 'yan bindiga suka kai a wata coci. Ta sha alwashin cewa za ta ceto mutanen da 'yan bindigan suka sace.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya nuna takaicinsa kan harin 'yan bindiga a Kano. Ya bukaci jami'an tsaro su tashi tsaye.
Kungiyar likitoci masu neman kwaewar aiki ta dakatar da yajin aikinta bayan kwanaki 29, inda ta bai wa gwamnati makonni hudu don aiwatar da bukatunta 19.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, na shirin sake tsayawa takara a zaben 2027. Ya fara zawarcin wanda za su yi takara tare.
Iyalan gidan sarauta sun tabbatar da rasuwar Sarkin Igbajo na 30 kuma tsohon shugaban APC na jihar Ogun, Oba Adegboyega Famodun, ya mutu ne ranar Juma'a.
'Yan bindiva dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kano. Tsagerun aun yi kisa tare da sace wasu mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna damuwa kan matsalolin rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce lissafo abubuwan da ke rura wutar matsalar.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta nuna damuwarta kan sunayen da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya turawa majalisa don tantancewa su zama jakadu.
Gwamnan Delta da wasu manyan jiga-jigai a jihar Delta sun halarci jana'izar tsohon gwamna a lokacin mulkin sojoji, Paul Ufuoma Omu a wata coci yau Asabar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari