Manyan Labarai A Yau
Majalisar wakilan Najeriya ta sanar da lokacin da kada kuri'a kan yi wa kundin tsarin mulki garambawul. Akwai kudurori da dama da ke neman yi masa garambawul.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ya nuna kaduwarsa kan mutanen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin jakadu.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da manoman da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Kaduna. Sun tafi da su zuwa cikin daji.
Gwamna Biodun Oyebanji ya dawo da galibin kwamishinonin da ya kora domin dinke barakar da ka iya barkewa a jam'iyyar APC kafin zaben gwamna a 2026.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa rikicin Boko Haram ba na addini ba ne. Gwamnan ya ce Musulmai da Kirista sun sha wuya kan rikicin.
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta mika kokon bararta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ta bukaci ya ceto adawa a Najeriya daga durkushewa.
Gwamnatin jihar Nasarawa ta nuna aniyarta ta kafa rundunar 'yan sandan jiha. Gwamnatin ta ce za a kafa rundunar ne domin tabbatar da tsaron al'umma.
Gwamnonin jihohin Arewa sun gudanar da taro kan matsalar rashin tsaro. Sun samo hanyoyin da suke son abi domin kawo karshen matsalar da ta addabi yankin.
Wasu matafiya a cikin motoci da dama sun tsinci kansu cikin musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da jami'an 'yan sanda a jihar Kogi. Sun nemi a kai musu dauki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari