Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani tantitin jagoran 'yan bindiga a jihar Sokoto. Sojojin sun kashe jagoran 'yan bindigan ne yayin artabu.
Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da karin albashi mai tsoka ga likitoci da ma'aikatan lafiya a fadin jihar. Ta amince da karin ne domin bunkasa ayyukansu.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC ta bayyana cewa har yanzu Abubakar Malami bai cika sharuddan da aka gindaya masa lokacin da aka ba da belinsa ba.
Jam'iyyar ADC ta ce soke belin Abubakar Malamai na iya sa mutane au zargi EFCV da goyon bayan wani bangare musamman yadda ya fara gangamin siyasa a Kebbi.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar goyon bayan da ya ba Shugaba Bola Tinubu ba a 2022.
Shugaban karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, Abubakar Umar Faru, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro. Ya ce sojoji na bukatar manyan makamai.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya samu mukamin sarautar gargajiya a jihar Benue. Mai martaba Tor Tiv zai nada masa rawani.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna goyon bayansa ga tsarin wa'adi daya a kan mulki. Ya ce zai taimaka wajen tabbatar da jagoranci mai kyau.
An sake taso da batun mutumin da zai yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu mataimaki a zaben shekarar 2027. Wasu na ganin cewa ba za a tafi da Shettima ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari