Manyan Labarai A Yau
Tsohon sanatan Zamfara ta Arewa, Kabiru Marafa, ya ragargaji karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle. Ya bayyana irin taimakon da ya yi masa wajen zama gwamna.
Gwamnan jihar Radda, Umaru Dikko Radda, ya amince a rika biyan malaman da ke koyarwa a yankunan karkasar alawus. An fito da tsarin ne domin karfafa musu gwiwa.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya nuna goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027. Ya ce zai mara masa baya.
Jita-jitar komawar Gwamna Abba da Rabiu Kwankwaso zuwa APC na kara karfi, yayin da masana ke gargadin cewa matakin zai canza taswirar siyasar Kano kafin 2027.
Shugaban kungiyar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya yi zarge-zarge kan matsalar rashin tsaro. Ya nuna cewa gwamnati na da masaniya kan matsalar.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka kan halin da 'yan siyasa ke nuna a Najeriya. Ya bayyana cewa sun dauki mukaman gwamnati daga su sai 'ya'yansu.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya yi hasashe kan kuri'un da Mai girma Bola Tinubu zai samu a Arewacin Najeriya a zaben shekarar 2027.
Yan Majalisa sun kaure da hayaniya da muhawara mai zafi yayin da aka gabatar da wani kudirida ya nemi a gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake tabo batun janye 'yan sanda daga gadin manya. Shugaba Tinubu ya nuna cewa ba gudu ba ja da baya kan umarnin da ya bayar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari