
Maiduguri







'Yan ta'addar Boko Haram sun kai mummunan hari jihar Borno sun kashe manoma 40. Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi kan mai uwa da wabi yayin harin.

Mayakan Boko Haram sun kai hari a ofishin 'yan sanda na Borno inda suka kashe jami'ai biyu. An ce wasu gurnetin hannu biyu da mayakan suka jefa ya yi kashe jami'an.

Sanata Ali Ndume ya ziyarci dakarun sojojin Najeriya da suka kashe 'yan boko Haram da dama. Ya raba tallafi ga mutanen mazabarsa da harin ya shafa.

Shugaban majalisar Borno, Abdulkarim Lawan, ya bukaci kafa rundunar soja a Guzamala da Kukawa don ’yantar da yankin daga Boko Haram tare da dawo da zaman lafiya.

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Kashim.Ibrahim, ya kuma ba da umarnin raɗawa tituna sunaye.

ISWAP ta kai hari kan sansanin soja a Damboa, ta kashe sojoji shida, ta banka wa sansanin wuta. Rikicin na tun 2009 ya halaka mutane 40,000 da raba miliyan biyu.

Gwamna Zulum ya rattaba hannu kan kasafin N615.857bn. Ya yaba wa majalisar dokoki, kuma ya sanar da nadin Dr. Mallumbe a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.

Gwaman Babagana Zulum na jihar Borno zai siyarwa da manoma man fetur kan N600 duk lita domin rage mu su radadin da suke ciki na matsalar Boko Haram.

Rundunar tsaron Najeriya ta karyata jita jitar cewa sojojin Faransa sun shigo Maiduguri na jihar Borno domin kafa sansanin soji. Sojojin sun ce labarin karya ne.
Maiduguri
Samu kari