Kannywood
An tafka rashe-rashe a masana'antar Kannywwod a 2024. Akwai rasuwar manyan jaruman da tsakaninsu bai wuce mak 2 ba. Mutuwar jaruman ta girgiza masana'antar.
Rayya Kwana Casa’in ta saki hotuna don murnar ranar haihuwarta, sun jawo ce-ce-ku-ce yayin da wasu suka yi fatan alheri, wasu kuma suka nuna rashin jin dadi.
Jami'ar Sule Lamido ta amince da nazarin wakokin Nura M Inuwa. Mawakin ya bayyana wakokin da za a bincika, ciki har da "Hindu" da "Bakin Alkami."
Kannywood ta yi rashin jarumi Baba Ahmadu (Hedimasta) na shirin Dadin Kowa. 'Yan Kannywood sun fito sun yi ta’aziyya, suna fatan Aljanna ce makomarsa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi rabon mukamai a gwamnatinsa. Gwamnan ya yi nade nade ciki har da na jarumin masana'antar Kannywood, Sani Danja.
Mawaki Abdul Respect ya angwance da Hassana Abubakar a Kano. Shahararrun mawaka da jarumai kamar Ado Gwanja, Momee Gombe, da Ali Nuhu sun halarci bikin.
Jarumai mata da maza sun cika wajen bikin diyar Asma'u Sani, suna wasa, dariya, da daukar hotuna a ranar daura aure, wanda ya kayatar kwarai da gaske.
Za a dawo haska shirin Gidan Badamasi zango na shida daga ranar 19 Disambar 2024, da misalin 6:00 na yamma, tare da barkwanci da salo mai ban sha'awa.
Hadiza Gabon ta tuna marigayi El-Muaz, wanda ya rasu a bikin mawaki Auta Waziri, tana cewa radadin rashin mutanen kirki baya gushewa daga zuciya.
Kannywood
Samu kari