Inna'lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Jarumin Wasan Barkwanci Sa’adu Bawo Ya Kwanta Dama

Inna'lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Jarumin Wasan Barkwanci Sa’adu Bawo Ya Kwanta Dama

  • Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta rasa daya daga cikin jarumanta na bangaren barkwanci
  • Allah Ya Yiwa Sa’adu Ado Gano wanda aka fi sani da Bawo rasuwa a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba
  • Marigayin na cikin yan farko da suka fara wasan barkwanci da jagoransu marigayi Rabilu Musa Ibro

Kano - Shahararren jarumin nan na masa’antar Kannywood a bangaren wasan barkwanci, Sa’adu Ado Gano wanda aka fi sani da Bawo ya rasu.

Kamar yadda fitaccen jarumin masa’anatar, Ali Nuhu ya bayyana a shafinsa na Instagram, Bawo ya rasu ne a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Gano Kan Hanyar Wudil.

Sa'adu Bawo
Inna'lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Jarumin Wasan Barkwanci Sa’adu Bawo Ya Kwanta Dama Hoto: realalinuhu
Asali: Instagram

Tuni dai aka yi jana’izarsa daidai da koyarwar addinin Musulunci inda aka sada shi da gidansa na gaskiya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Kudu Sun Sake Zama, Sun Yanke Wanda Zasu Goyi Bayan Ya Gaji Buhari a 2023

Marigayi Bawo dai yana daya daga cikin Manyan Jaruman Barkwanci wanda suke gudanar da harkokinsu na wasan barkwanci tare da marigayi Rabilu Musa ibro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan rasuwar Dan Ibro, harkar wasan barkwanci ya ja baya sosai kasancewar shine babban jigon tafiyar sannan kuma yan wasan bangaren da dama sun kwanta dama.

Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa cewa:

“Inna'lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,, ALLAH Yayiwa Dan Wasan Barkwanci, SA'ADU, Wanda Akafi Sani da {BAWO} Rasuwa Yau a Gidansa Dake GANO Kan Hanyar WUDIL, ALLAH Yajikansa Yayi Masa Rahama Ameen .”

Jama’a sun mika ta’aziyyarsu

Tuni mabiya shafinsa suka fara kwararo sakonnin ta’aziya ga masana’antar ta Kannywood kan wannan rashi da aka yi.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sakonninsu a kasa:

abdul_d_malan ya yi martani:

"Allah yajikansa."

asp_lamari02 ya ce:

“Amin Allah ya jikan,sa da Rahma Amen”

Kara karanta wannan

Hotuna Daga Shagalin Bikin Jarumar Kannywood, Halima Atete, Jama'a Sun Yi Martani

a_a_bash__ ya rubuta:

“Rahimahullah ”

hadeezaswaleeh ta yi addu’a:

“Allah ya jikan sa da Rahama.”

ruqayyataa88 ta ce:

“Allah ya jikanshi ya kyauta namu karshen ”

excellency_ysg ya rubuta:

“Allah Yaji kanshi Allah yasa yahuta. Allah yasa Asamu wanda kula da masa da iyali ameen .”

anchuchi ta ce:

"Allah ya jikan shi da rahma ."

mks_decorium ta rubuta:

"Allahumma ghafir wa Rahman ."

el_khaleel_muhammad ya yi addu'a:

"Rahimahullah "

Asali: Legit.ng

Online view pixel