Gaskiyar abun da ya raba aurena da Fati Mohd – Sani Musa Mai Iska

Gaskiyar abun da ya raba aurena da Fati Mohd – Sani Musa Mai Iska

  • Tsohon jarumin Kannywood, Sani Musa Mai Iska ya yi tsokaci a kan rabuwar aurensa da jaruma Fati Mohammad
  • Mai Iska ya ce babban abun da ya kawo rabuwar aurensu da Fati shine ta saka soyayyar mahaifiyarta a gaba yayin da shi kuma ya saka na karatunsa a gaba
  • Ya kuma jadadda cewa saki biyu ya yi mata inda ita kuma ta nunawa duniya cewa saki uku ya yi mata

Tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa kuma miji ga tsohuwar jaruma, Fati Muhammad, Sani Musa Mai Iska ya magantu a kan abun da ya kawo rabuwar aurensu a shekarun baya.

Mai Iska ya tuno yadda aurensu ta kasance da Fati wacce suka lula suka bar kasar zuwa Ingila yan watanni bayan bikin nasu sakamakon samun damar shiga wani shiri na wayar da kai kan Kanjamau da ita jarumar ta yi.

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

Jarumin ya ce bayan sun je kasar Ingila sun kammala shirin, sai suka dawo gida Najeriya amma sai shi ya sake komawa kasar saboda wani dalili nasa na gashin kansa. Ana haka sai ya ga cewa zai fi samun nutsuwa idan matarsa na kusa da shi don haka ya nemi Fati ta dawo kasar ita ma.

Ba laifinta bane: Sani Mai Iska ya bayyana gaskiyar abun da ya raba aurensa da Fati Mohammad
Ba laifinta bane: Sani Mai Iska ya bayyana gaskiyar abun da ya raba aurensa da Fati Mohammad Hoto: NAIJASTICK/BBC Hausa
Asali: UGC

Bayan sun yi zama na shekaru uku, sai ya zamana hankalinta ya koma wajen mahaifiyarta da ke gida Najeriya inda shi kuma ya ga ba zai iya barin karatunsa ya koma gida ba saboda ya yi nisa a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hirar da aka yi da shi a wani shiri na sashin Hausa na BBC mai suna ‘Daga bakin mai ita’, an jiyo Sani Mai Iska yana cewa:

“Tana da gaskiya ina da gaskiya. Uzurinta a wancan lokacin mahaifiyarta da mahaifinta musamman ma mahaifiyarta Allah ya ji kansu dukkansu sun rasu. Ni kuma uzurina dama ban kammala babban sakandare ba toh kuma ga dama ta samu, ina ga ya kamata na tsaya na samu dan wani abu. Toh wannan shine babban abun, ya zamana ni ba zan janye karatuna ba kuma na yi nisa, ita kuma tana matukar kaunar mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Dala 500k/N220m: Tulin miliyoyin da dan Najeriya ya kai banki zai ajiye ya girgiza jama'a

“Saboda haka sai muka je muka sami su hukumomi muka ce masu toh gashi gashi, sai su Uk suka bamu zabi cewa tana da zama za mu iya mu raba aurenmu amma za ta iya tafiya inda take so ta je ni kuma zan iya zama a inda nake so na zauna har sai na kammala abun da nake so.
“Amma akwai rudani a cikin lamarin saboda shi abu idan aka ce maka musamman ita a lokacin nan wato tauraruwarta tana haskawa sosai, Allah ya daukake ta sosai ta kowani bangare don ko a can UK din ta samu soyayya daga bangare daban-daban. Ta sanadiyarta ne ma nima na san wasu manyan wurare daban-daban.
“Ni a alkalancina Fati ba laifinta bane, Allah ne ya kawo kaddara, dama shi da aure da saki wani abu ne duk kamar guda daya, sai muka yanke shawara cewa zan maki saki daya amma bazan yi maki a nan ba, sai na tabbatar kin isa gida Najeriya lafiya kin hadu da yan uwa sai a tattauna. Kuma abun da aka yi kenan.

Kara karanta wannan

Yadda Matashiya Mai Shekaru 34 Ta Biya Sadakin Aurenta Da Kanta

"Toh amma, sai ya zamana an samu wasu sun ba da gudunmawa, sai ya zamana kafin tawowarta kuma sai aka dauki cewa na saketa saki uku.”

Da BBC ta tambaye shi kan ko za su iya dawo da aurensu kasancewar saki daya ya yi mata, sai Sani ya ce:

"Ba saki daya bane, saki biyu ne amma ita kuma ta kai shi uku kuma duniya ta tafi a kan ukun. Kuma ita rayuwa da kake gani yanzu ban san ainahin me take yi, ko me zata yi ko kuma menene shirinta a rayuwa ba kamar yadda nima bata sani ba."

Gaskiya ne abun da Mai Iska ya fada - Fati Muhammad

Wakiliyar Legit Hausa ta tuntubi Fati Muhammad domin jin ra'ayinta game da abunda tsohon mijin nata ya fadi na cewar kowannensu na da gaskiya a rabuwarsu, inda ta bayyana cewa tabbass abun da ya fadi gaskiya ne ta ce:

Kara karanta wannan

Dambe Ya Kaure Tsakanin Ango Da Wani Mutum Da Ya Lika Masa Kudi a Wajen Shagalin Bikinsa, Bidiyon Ya Yadu

"Gaskiya abunda ya fada hana ne."

Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba – Lawan Ahmad

A wani labarin, shahararren jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa ya taba soyayya da tsohuwar jarumar masana’antar, Fati Muhammad a shekarun baya.

Lawan ya ce a wancan lokacin har magana ta yi karfi tsakaninsu, domin manya sun shiga lamarin ana ta maganar aure.

Sai dai kuma jarumin ya ce ana tsaka da maganar auren ne sai maganar ta wargaje domin Allah bai yi za su zama mata da miji ba. Ya kuma ce tun bayan ita bai kara soyayya da wata yar fim ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel