An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu

An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta saki sabbin sunaye na ‘ya’yan kwamitin yakin neman zabenta na shugaban kasa
  • A wannan karon ma wasu jaruman masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood sun samu shiga jerin
  • Sai dai kuma, ko sama ko kasa ba a ga sunan shahararran mawaki Daudu Kahutu Rarara ba wanda a da yana cikin kwamitin

Jam’iyyar APC ta saki sabbin sunaye na mambobin kwamitin yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan ta yi yan gyare-gyare a wanda ta fitar a baya.

Har yanzu shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakalla na nan a matsayin mataimakin darakta a bangaren masu nishadantarwa na kwamitin kuma zai jagorancin yankin arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Sunayen da Aka Kara da Wadanda Aka yi Watsi da su a Kwamitin Neman Takarar Tinubu

Rarara
An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jarumi Nuhu Abdullahi na nan a matsayinsa na mataimakin mai kula da jin dadin kwamitin yan wasan. Sani Idris Moda ma yana nan a cikin kwamitin.

Sai dai kuma, a wannan karon, ba a ga sunan shahararren mawakin siyasa, Daudu Kahutu Rarara ba a cikin wanda a da shine ke rike da mukamin jami’in kula da harkokin kwamitin na yan wasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Rarara ya saki sabuwar waka inda ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano.

A cikin sabuwar wakar da ya fitar don yi wa Tinubu kamfen, Rarara ya tabbatar da rikicinsa da Ganduje kuma ya bayyana gwamnan a matsayin 'Hankaka', ma'ana mutum mai fuska biyu.

Rarara kuma ya zargi Ganduje da daƙile saka sunansa a kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

A wani labarin, wata kungiyar goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai suna Jagaban National Coalition ta fara bi gida-gida tana yi masa kamfen.

Jagoran kungiyar a jihar Plateau, Mista Zakariyau Adigun, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a garin Jos, a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba.

Adigun ya ce shirin kungiyar shine sanar da duk wani dan jihar nasarorin Tinubu da kyawawan shirin da yake yiwa kasar, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel