Alkawarin Aure: Kotun Musulunci Ta Dauki Wani Mataki Kan Shari'ar Hadiza Gabon

Alkawarin Aure: Kotun Musulunci Ta Dauki Wani Mataki Kan Shari'ar Hadiza Gabon

  • Kotu dake sauraron ƙarar Alkawarin aure da Jaruma Hadiza Gabon ta ɗage zaman zuwa 15 ga wannan watan bayan ɗaukar wani mataki
  • Alkalin Kotun ya amince da bukatar wani babban lauya na shiga tsakanin mutanen biyu domin yin sulhu
  • Bala Usman ya kai ƙarar Gabon ne bisa tuhumar gaza cika masa alƙawarin aruen data ɗauka bayan kashe mata kudade

Kaduna - Kotun Shari'a dake zamanta a Magajin Gari Kaduna ta ɗage zaman shari'ar Fitacciyar Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba, 2022.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kotun ta ɗauki wannan matakin ne domin bangarorin biyu su je su yi sulhu tsakaninsu a wajen Kotu.

Jaruma Hadiza Gabon.
Alkawarin Aure: Kotun Musulunci Ta Dauki Wani Mataki Kan Shari'ar Hadiza Gabon Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Idan baku manta ba, Bala Usman, wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a gaban Kotu bisa zargin ta saɓa alkawarin auren da ta masa bayan kashe mata N396,000.

Kara karanta wannan

'Na Gaji da Wannan Auren A Raba Mu' Wata Mata Ta Fada Wa Kotun Musulunci Cin Kashin da Mijinta Ke Mata

A cewarsa ya jima yana soyayya da jarumar har ta masa Alƙawarin aure. Zargin da Gabon ta musanta da cewa ba ta taɓa ganin shi ba a rayuwarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda zaman Kotun ya gudana ranar Laraba

Alƙalin Kotun mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, a ranar Laraba, ya ɗage zaman bayan wani babban Lauya, Suleiman Lere, ya roki Kotun ta bashi lokacin ya shiga tsakanin mutanen biyu domin sulhu.

Lauyan mai ƙara, Barista Nuruddeen Murtala, ya yi na'am da shirin sulhun da babban Lauyan ya kawo, inda ya ƙara da cewa Sulhu alkhairi ne da Allah SWT ke so saboda haka basu da jayayya.

A ɓangarensa lauyan wacce ake ƙara, Barista Mubarak Sani, ya amince da shirin sulhun amma ya nemi Kotu ta fara sauraron shaidun da ɓangaren masu kara suka yi alƙawarin zasu gabatar.

A wani labarin kuma wani magidanci ya garzaya Kotu neman saki, ya labarta wa Alkali yadda ya kama matarsa tana lalata da ɗan uwansa

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Rikicin Tsagewa Biyu, Uwar Jam'iyya Ta Kasa Ta Nada Sabon Shugaban PDP a Katsina

Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ya nemi wata Kotu a Abuja ta raba aurensa da Joyce bisa zargin ganinta ta kwanta da ɗan uwansa.

Mutumin ya faɗa wa Alkali cewa matar bata kula da shi, yayansa da sauran iyalai, burinta kawai ta kwanta kowa ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel