Ana Tsaka Da Shagalin Biki An Fasawa Amarya Ido a Jihar Kano

Ana Tsaka Da Shagalin Biki An Fasawa Amarya Ido a Jihar Kano

  • Rikici ya barke wajen taron shagalin biki a jihar Kano kuma tsautsayi ya fada kan Amaryar bikin
  • Jami'an yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu cikin tada rikicin a wajen bikin
  • Angon ya lashi takobin cewa ba zai yarda ba sai an hukunta dukkan masu hannu cikin wannan abu

Kano - A ranar da ya kamata ya zama mafi muhimmanci da farin ciki a rayuwar Amarya da Ango a jihar Kano, an fasawa Amarya ido yayinda rikici ya barke ana tsaka da shagalin biki.

Amaryar mai suna Khadija Abdullahi, ana fargaban ta rasa idonta daya yanzu bayan jifar dutsen da akayi kuma yayi sanadiyar hakan.

BBC ta ruwaito cewa wannan shagalin aure ya gudana ne a unguwar Kwalajawa dake jihar Kano.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Kama Jarumin da ya Caka wa Makwabcinsa Wuka a Kirji kan N1,000

Angon Hamza Bala ya bayyana cewa shi dai ba zai yarda ba kuma wajibi ne a kwatowa Amaryarsa hakkinta.

Amaryata
Ana Tsaka Da Shagalin Biki An Fasawa Amarya Ido a Jihar Kano Hoto: Rabiu Arewa/BBC
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace:

"Amaryata da kawayenta sun shirya shagali inda aka gayyaci DJ na daurin auren mu. Lokaci guda sai yan bijilante suka dira wajen."
"Sai na samu labarin Amaryata ta sume kuma an kaita asibiti. Kai tsaye na tafi wajen domin ganewa idona abinda ya faru kuma da na isa wajen na samu labarin jifanta akayi da dutse."
"Bayan da ta farfado, an kai mu wajen Likitocin Ido kuma suka sanya mata bandaji a ido."

Hamza ya ce yanzu kawai abinda yake so shine a hukunta wadanda suka aikatawa amaryarsa haka.

A cewarsa:

"Kawo yanzu yan sanda sun kama mutum biyu. A fadar Amaryata kawai tsautsayi ya hau."
"Wannan mumunan abu ne saboda ranar da ya kamata ya zama na farin ciki ya zama na bakin ciki."

Kara karanta wannan

Ba a Afrika kadai bane: Kamar dai na ASUU, malamai a Ingila za su shiga yajin aiki

Hamza ya ce har yanzu tana asibiti kuma Likita ya basu tabbacin cewa da yardan Allah zata sake gani da idon.

Ko ta rasa idon ba zan daina son ta ba

Hamza ya bayyanawa BBC cewa ko kadan wannan abu da ya faru ba zai rage masa soyayyan da yake mata ba.

Yayinda aka tambayesa wani tasiri hakan zai ga soyayyarsu, yace:

"Ko kadan. Zan so ta hakan. Abinda ya faru kaddara ne saboda haka babu abinda zai rage soyayyar da nike mata."

Asali: Legit.ng

Online view pixel