2023: Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Kannywood da Kyautar N50m

2023: Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Kannywood da Kyautar N50m

  • Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa masana’antar Kannywood kyautar naira miliyan hamsin
  • Wannan ya faru ne a ranar Lahadi yayin da Tinubu ya halarci gagarumin taron da masana’antar ya shirya masa a garin Kano inda suka kayatar da shi
  • Shugaban MOPPAN na kasa, Dakta Sarari, ya bayyana masana’antar a matsayin wurin samarwa matasa aiki da kudin shiga

Kano - Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya gwangwaje masana’antar Kannywood da gudumawar N50 miliyan domin cigaban masana’antar.

Tinubu da ‘yan fim
2023: Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Kannywood da Kyautar N50m. Hoto daga fimmagazine.con
Asali: UGC

Mujallar fim ta rahoto cewa, Tinubu ya bayar da wannan makuden kudaden ne a yayin da ya halarci taro na musamman da ‘yan fim suka hada masa a daren Lahadi a fadar gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

A yayin jawabi kan manufar taron, Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wannan taron na matasan fim ne masu goyon bayan Tinubu. Sun shirya shi a karkashin gidauniyar Kannywood don su nuna yadda karfin goyon bayan da yake da shi a wurin ‘yan fim.
“A saboda Haka a shirye suke domin bashi dukkan goyon baya don ganin ya kai ga nasara.”

A jawabin shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Najeriya, MOPPAN na kasa, Dakota Ahmad Sarari, ya sanar da cewa Kannywood a matsayin babbar masana’antar da ke kawo kudin shiga da aikin yi ga matasa.

Don haka yayi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar take idan ya samu cin zabe.

A jawabin tsohon shugaban MOPPAN kuma jarumin fim, Alhami Sani Mu’azu, yayi kira ga Tinubu da ya zuba ‘yan masana’antar a cikin yakin neman zabensa saboda masoyan da suke da shi da kuma jama’a.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Yayin mayar da martani, Gwamna Samuel Lalong, shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu na kasa ya sanar da su cewa daman suna cikin tafiyar dumu-dumu.

Hakazalika, ya sanar da gudumawar naira miliyan hamsin da Tinubu ya bai wa masana’antar domin inganta ta.

Jama’ar da suka halarci muhimmin taron sun hada da dukkan kungiyoyin dake masana’antar.

Mansurah ga Tinubu: Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin kasan Abj-Kd

A wani labari na daban, Ba a bar jaruman Kannywood a baya ba, jarumai irinsu Ali Nuhu da Mansurah Isah sun bayyana tashin hankalinsu.

Wallafar Mansurah Isah ta ja hankalin jama'a inda tayi kira ga 'dan takara shugabancin kasa na jam'iyya APC, Bola Ahmed Tinubu da yayi wani abu, ita kuma zata masa kamfen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel