Sharhin Malamin Addinin Musulunci Kan Kannywood Ya Tayar da Hankula

Sharhin Malamin Addinin Musulunci Kan Kannywood Ya Tayar da Hankula

  • Wani fitaccen malamin addinin Islama, Dr Idris Abdulazeez ya tada kura bayan yayi wani furuci game da 'yan wasan kwaikwayo na masana'antar Kannywood
  • Kamar yadda wani bidiyon wa'azin malamin da yayi tashe a soshiyal midiya ya nuna, an gansa yana cewa jaruman masana'antar basa da rike addini
  • Yayin da wasu daga cikin jaruman suka fito fili suna kalubanci ra'ayin malamin, wasu daga cikinsu sun amince da hakan gami da zargin masu musanta batun da son zuciya

Tsokacin da fitaccen malamin addinin Islama, Dr Idris Abdulazeez yayi kan 'yan wasan kwaikwayon Kannywood ya tada kura cikin masoyan masana'antar fina-finan Hausa da 'yan wasan kwaikwayon.

Kannywood
Sharhin Malamin Addinin Musulunci Kan Kannywood Ya Tayar da Hankula. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Malamin addinin da ke zaune a Bauchi, a daya daga cikin wa'azozinsa, ya ce 'yan fim basa da riko da addini.

An fara martani

Kara karanta wannan

Ina Biyan Kudin Haya N800k Duk Shekara: Budurwa Ta Nuna Cikin Dakinta Da ke Da Wuta 24/7

Yayin da bidiyon wa'azin malamin yayi yawo a duk kafafan sada zumuntar zamani, wasu daga cikin 'yan wasan kwaikwayon sun fara martani game da ra'ayinsa da ya bayyana karara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, wanda bai cika shiga lamurran da suka shafi masana'antar a soshiyal midiya ba, yayi bidiyo inda yake sukar ra'ayin malamin.

Sadiq ya ce, yana alfahari idan aka alakanta shi da masana'antar shirya fina-finai kuma yana fatan cigaba da rayuwarsa a matsayin jarumin masana'antar har karshen rayuwarsa.

"Abun takaici ne a ce irin wadannan lafuzzan suna fitowa daga wani da yake ikirarin shi malamin addini ne. Na kai inda nake a yau ne saboda wasan kwaikwayo, kuma a shirye nake da in bar 'ya'yana su gaje ni idan suna da burin hakan.
"Zan cigaba da kasancewa jarumin wasan kwaikwayo har karshen numfashina. Ba na da na sanin kasancewana a Kannywood."

Kara karanta wannan

Assha: Ba a gama da jimamin Hanifa ba, wasu matasa sun sace yarinya mai shekaru 6 a Kano

- A cewarsa.

Wani jarumi kuma mawaki a masana'antar, Musbahu M. Ahmad, shima yayi bidiyo inda yake kalubalantar malamin bisa yin katsalandan ga masana'antar. A cewarsa, furucin malamin bai kyautu ba, sannan bai dace da koyarwar addinin Islama ba.

"Ka na so mu kawo maka malamin addini ne? Me za ka yi da shi ko ita? Mun ji babu dadi da yadda wadannan lafuzzan ke fitowa daga bakin wani da yake ikirarin shi malamin addini ne.
"Zan bada shawara cewa Sheikh ya mayar da hankali kan da'awa ba abun da yake yi cikin kwanakin nan ba,"

- Cewar Ahmad.

Wasu jaruman sun goyi bayan Malamin

Sai dai, ba kamar sauran jaruman ba, Adam A. Zango ya ce bai kamata a kalubalanci maganar malamin gaba daya ba, saboda ya kamata jaruman su canza dabi'unsu.

"Dabi'u da halayenmu, musamman a soshiyal midiya sun bada damar fassara da daukar masana'antar a wani abu daban. Bai dace mu kushe malamin kai tsaye ba, sai dai mu duba mu kuma gyara kuskurenmu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

"Maganar gaskiya, masana'antar na bukatar gyara. Sama da shekaru 10, na dade ina rokon Ubangiji ya kawo min sauyin sana'a idan wasan kwaikwayo ba shi bane alheri gare ni, sai dai ya cigaba da kara min daukaka a cikinta."

- A cewar Zango.

Wani jarumi da ke zaune a Jos, JBoy, ya ce, malamin addinin bai yi kuskure ba su kuma wadanda suke sukarsa su na yin hakan ne saboda son zuciya. A cewarsa, Kannywood ta zama matattarar duk wasu munanan halaye, inda ya kara da cewa gaskiya ne 'yan wasan kwaikwayon basa da riko da addini.

"Ya kamata mu fadawa kanmu gaskiya - Muna kauce hanya kuma babu wanda zai iya goge hakan a idon duniya.
"Masana'antar tabbas ta cika da mutane daban-daban masu duk wasu munanan halaye da ke bukatar addu'a. Abun da malamin ya ce shi ne gaskiya kuma ya kamata mu yarda da hakan yadda yake.

Kara karanta wannan

2023: Atiku da PDP Sun Samu Goyon Bayan Manoma Daga Jihohi 7 a Arewa

"Ina rokon Ubangiji ya albarkace ni da wata sana'a mai tsafta yadda zan bar wannan fannin. Ubangiji ya san ba dai-dai muke yi ba."

- A cewarsa.

Tun daga lokacin da bidiyon wa'azin malamin yayi yawo, mutane da dama sun tsunduma cikin muhawara game da maudu'in - yayin da wasu suke marawa maganarsa baya, wasu kuwa sukar ra'ayinsa suke game da 'yan wasan kwaikwayon.

Sai dai a sabon bidiyo, malamin ya tsaya kan bakarsa gami da addu'ar shiriya ga wadanda ke kalubalantar ra'ayinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel