Shahararren Mawakin Najeriya Zai Daina Waka, Zai Zama Makarancin Kur’anin Duniya

Shahararren Mawakin Najeriya Zai Daina Waka, Zai Zama Makarancin Kur’anin Duniya

  • Aliyu Isa watau Ali Jita ya bada sanarwa a shafinsa na Twitter cewa ya kusa daina harkar wake-wake
  • Mawakin da ‘yan mata ke sha’awar wakokinsa ya ce burinsa shi ne ya zama makarancin Al-Kur’ani
  • Ali Jita yana so yadda ya shahara da waka, ya zama daya daga cikin kwararrun masu karatun Kur’ani

Abuja - Fitaccen mawakin nan kuma ‘dan wasan kwaikwayo, Aliyu Isa wanda aka fi sani da Ali Jita ya sanar da Duniya niyyarsa na daina yin waka.

A ranar Laraba, 11 ga watan Junairu 2023 da kimanin karfe 12:00 na rana, Ali Jita ya ba mabiyansa a Twitter mamaki, ya fada masu ritaya daga wakoki.

Bai fadi takamaimen lokaci ba, amma mawakin ya ce nan gaba zai zama makarancin Al-Kur’ani.

"Kamar yada ya shaida a shafinsa, burin Ali Jita mai shekara 39 a Duniya shi ne ya zama daya cikin kwararrun makarantar littafin mai tsarki a duk Duniya.

Kara karanta wannan

Dan Mai Karfi: Bakanike Mai Daukar Injin Mota Shi Kadai Ya Bayyana a Bidiyo

Ba da dadewa ba, zan yi ritaya daga wake-wake."
Idan Allah ya so, nan gaba ina so in zan zama daya cikin masu mafi dadin sautin karanta Kur’ani da aka taba yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Ali Jita

Mawakin Najeriya
Ali Jita rike da kayan aiki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mutane fiye da 80, 000 ne suke bibiyar mawakin na jihar Kano wanda ya kware a rangada murya da rubuta wakoki a dandalin sada zumuntan.

Wasu da-dama sun yi farin-ciki da jin labarin, suka shiga yi wa tauraron fatan alheri.

Mutane sun yi maraba da labarin

Legit.ng Hausa ta bibiyi martanin jama’a, ta ji wasu na cewa Ali Jita zai dace da makarancin Al-Kur’ani saboda baiwar muryar da yake da shi.

Malam AbdusSami' Abu AbdiLLAH ya yi wa mawakin addu’ar cewa Allah ya biya masa bukatarsa, ya ba shi ikon yin riko da sunnar Annabi SAW.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

Ita kuma wata Chef Adylerh Noorieee tana nemen alfarma ne Ali Jita ya rera mata waka kafin lokacin da zai yi watsi da jitarsa, ya zama Alaranma.

Shi Malam Sabiu Zaranda cewa ya yi Allah ya saukake masa burinsa, ya tsarkake masa zuciya.

Akwai wani iRasheed da ya fadawa ‘dan wasan ya hadu da shehin malamin Kur’ani, Dr. Jamilu Muhammad Sadis domin ya ba shi shawarwari.

Shari'ar 'Dan China a Kano

Da aka koma kotu a makon nan, an ji labari Frank Quanrong ya jero kudin da yake ikirarin ya kashewa Ummulkutum Buhari watau Ummita.

Quanrong ya ce a lokacin da suke soyayya da wanda ake zargin ya kashe, ba ta jarin N18m, kuma ya saya mata gida, mota da wayoyi na miliyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel