Gaskiyar Magana Game Da Jarumar Da Take Fitowa A Shirin Nan Mai Dogon Zango Na Amaryar Tik-Tok

Gaskiyar Magana Game Da Jarumar Da Take Fitowa A Shirin Nan Mai Dogon Zango Na Amaryar Tik-Tok

  • Masana'antar Kannywood na fuskantar matsal-tsalu iri-iri da suka hada hanyoyin shiga masana'antar da kuma wasu dokoki da suka shafi shigar ko fita
  • Wani zargi ne ya daibaibaye daya daga cikin jaruman da suke fitowa a daya daga cikin fina-finan masana'antar
  • Jarumar na fitowa ne a shirin nan mai dogon zango da ake kira da Amaryar Tik-Tok wanda ake dorawa a Facebook

Kano - Wani bidiyo ne ya karade shafukan sadarwa na zamani inda aka ga wata mata sanye da hijabi na rokan yan kannywood su bar mata yarta haka.

Amaryar
Gaskiyar Magana Game Da Jarumar Da Take Fitowa A Shirin Nan Mai Dogon Zangon Na Amaryar Tik-Tok Hoto: UCG
Asali: UGC

Bidiyon mai tsawon minti daya da doriya wanda wata mata ta bayyana a matsayin mahaifiyar Jarumar wanda sunanta na gaskiya shine Aisha Usman amma ana kiranta da Humaira.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kishi Kumallon Mata: Wata Mata Ta Kona Kishiyarta Da Wuta Har Lahira

Matar wadda tace sunanta Maryam tace:

"Dan Allah dan Annabi yan kannywood ku bar min yata haka, wallahi tana da aurenta, sannan kuma mune iyayenta, ni da babanta bamu san ta shiga flim ba, da mijinta ta tsallake ta barshi kuma ta shiga flim"

Martanin Humaira

A wata hira da Aisha tayi da gidan Radiyon Freedom dake kano, ta bayyanawa duniya cewa ba ita bace wadda ake cewa ta tsallake mijinta ta shiga harkar fim.

Tace ta samu labarin cewa ta tsallake mijinta da iyayenta cewa tashiga fim ba ita bace, tace ta samu labarin kamar yadda kowa ya samu, tace:

"Akwai wata jaruma da aka shigo da ita shirin kwanan nan to ita ce amma ba ita ba"

Ta ci gaba da cewa

"A matsayin daraktan fim din mai suna Ahmed Biffa ya kamata ya da ni komai cewa wannan jarumar da muke shiri da ita a cikin wannan shirin namu mai dogon zangon tana da aure."

Kara karanta wannan

Yadda Hannun Gajeruwar Yar Bautar Kasa Ya Gaza Kaiwa Saman Allo, Dalibai Sun Fashe Da Dariya a Bidiyo

"To tunda ya fada min jikina yayi sanyi kuma na ringa addu'a Allah ya kawo mana abin da sauki, to kasan kaddara, kawai sai ji nayi an ce ai ni ce ba waccar din da aka shigo da ita ba."
"Tace kawai ta tashi sai ta ga an turo mata bidiyon kuma taga ana ta kiranta a waya, ta ce harta mama na ma sai da aka tura mata, kuma tazo ta tambayeni, amma na fada mata ba ni bace daya jarumar ce dai."

Tace waccar matar sunanta Hafsa Ibrahim Tuge itace wadda akai wannan bidiyon akanta ba ita ba.

Baya ta haihu

A wani bidiyo da shafin kannywaood ya wallafa wanda ke dauke da bidiyon ita jarumar da ake cece-kuce a kanta.

Jarumar ta bayyana sunanta, kuma ta musanta zargin tana mai cewa ba gaskiya bane, kaman yadda zaku gani a bidiyon dake kasa.

Kara karanta wannan

Shekarunta 23: Wani Mutum Ya Wallafa Hotunansa Da Wata Mata Mai Nakasa, An ce Sun yi Aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel