Na Samu Juna Biyu: Ummi Rahab Ta Bukaci Masoyanta Su Taya ta Murna

Na Samu Juna Biyu: Ummi Rahab Ta Bukaci Masoyanta Su Taya ta Murna

  • Tsohuwar jarumar Kannywood kuma amaryar mawaki kuma furodusa, Shuaibu Ahmed Idris wanda aka fi sani da Lilin Baba, Ummi Rahab, ta samu juna biyu
  • Matashiyar ta sanar da hakan a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotonta tare da kira ga jama’a da su taya ta murna kan wannan nasarar
  • Amaryar Lilin Baba bata tsaya nan ba, tayi alkawarin gwangwaje mutane 50 na farko da suka fara taya ta murna da katin waya

Kaduna - Amaryar fitaccen mawaki sannan jarumi Shuaibu Ahmed Idris wanda aka fi sani da Lilin Baba, wacce ita ma tsohuwar jarumar Kannywood ce, Ummi Rahab, ta sanar da cewa tana dauke da juna biyu.

Ummi Rahab
Na Samu Juna Biyu: Ummi Rahab Ta Bukaci Masoyanta Su Taya ta Murna. Hoto daga @ummirahabofficial
Asali: Instagram

Amaryar ta bayar da wannan sanarwan ne a shafinta na Instagram inda ta saka hoton ta sanye da atamfa ja tana zaune a kujera cike da murmushi.

Jaridar Fim Magazine ta rahoto cewa, jarumar ta sanar da cewa tana dauke da juna biyu da harshen turanci.

Tayi Alkawarin Bada Kyautar Kati

Wallafar tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“I’m pregnant.” Hakan yana nufin “Ina dauke da juna biyu.”

Tsohuwar jarumar ta bukaci masoyanta da su taya ta da murna inda tayi alkawarin tukuicin katin waya ga mutum 50 na farko da suka fara saka sakon taya murna a kasan hotonta.

A cewarta:

“In har na samu tsokaci ta hanyar rubuta ‘Congratulations’ a karkashin wannan hoton, zan bada kyautar kati ga mutane 50.”

Sai dai kuma jarumar bata sanar da katin nawa zata bai wa kowanne mutum ba da yayi tsokaci.

Tsohuwar jarumar kuma amaryar Lilin Baba bata sanar da watannin cikin nata nawa ba.

Tuni dai masoyan tsohuwar jarumar suka dinga tururuwar taya ta murna tare da yi mata fatan alheri.

Auren Ummi da Lilin Baba

A ranar 18 ga watan Yunin 2022 aka daura aurenta da masoyinta Lilin Baba a Unguwar Tudun Murtala dake Kano a kan sadaki N200,000.

Fitaccen jarumi Ali Nuhu ne ya tsaya matsayin waliyyin ango kuma ya karba masa auren.

Soyayyar Lilin Baba da tsohuwar jarumar dai ta kasance abun sha’awa da kwatance a masana’antar tun bayan da lamarin ya fito fili.

Masoyan kan wallafa hotuna da bidiyoyin juna suna rangada kalaman soyayya da kauna a shafukansu na sada zumuntar zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel