Jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya sauya matakin da gwamnatin Nasir El-Rufai ta dauka na kwace filayen iyalan Sani Abacha guda biyu da ke cikin birnin Kaduna.
Alhaji Rabiu ya dauki nauyin sake gina masallacin Zariya, inda ya fara bayar da N2bn. Sabon masallacin zai iya daukar mutane 7,000 tare da kayan zamani.
Bayan kiran Sarki Muhammadu Sanusi II da tsohon sarki, Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya nemi afuwar al'umma musamman masoyansa kan kalaman da ya yi.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi rabon mukami a gwamnatinsa. Gwamna ya nada mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi.
‘Dan Ministan kasafin kudin Najeriya ya auri sahibarsa, Amina Tatari Ali a Kaduna. An daura auren Ibrahim A. Bagudu da Amina ne a masallacin nan na Sultan Bello.
Tsohon dan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya sake magana kan halin da matarsa ke ciki bayan hira ta musamman da kungiyar Ajax da ke kasar Netherlands.
Wata mata a Kaduna ta gurfana gaban kotu kan kashe diyarta da guba. Kotun ta umarci NSCDC ta tura fayil zuwa daraktan shari’a don shawara kan karar.
DJ AB ya gamu da fushin mabiyansa kan bidiyon haraji, wasu sun ce lokacin sakin bidiyon bai dace ba, yayin da wasu suka zazzage masa tare da yi masa barazana.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga kwanton bauna a jihar Kaduna. Sojojin sun kuma kwato shanun da aka sace a rugar Fulani.
Jihar Kaduna
Samu kari