Jihar Kano
A labarin nan, za a ji cewa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya samu goyon bayan fitaccen malami kuma tsohon 'dan takarar Gwamna, Sheikh Ibrahim Khalil.
Saƙonnin taya murna na cikar gwamna Abba Kabir Yusuf shekara 63 sun ƙunshi bayanan siyasa masu zurfi daga Ganduje da Kwankwaso, suna ɗauke da alamu na sauyin kawance
A labarin nan, za a ji cewa fitaccen dan siyasa a Kano, Garba Kore Dawakin Tofa ya ce akwai shirin Kwankwasiyya na hana Abba Kabir Yusuf takara a 2027.
Kotun jihar Kano ta dauki matakin rusa hukuncin shugabannin NNPP na kasa kan rusa shugabancin jihar Kano da suka yi bayan fara rikicin Abba Kabir da Kwankwaso.
Mataimakin shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Alhaji Sani Danmasani ya bayyana cewa Gwamma Abba Kabir ne jagoran jam'iyya ba Rabiu Musa Kwankwaso ba.
An kashe mutum ɗaya a wani rikicin daba da ya barke a Kano yayin da ’yan sanda suka kama mutum 9 a yankunan Kawo da Mariri bayan yunƙurin ɗaukar fansa.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekaru ya ce Kwankwaso ba shi da hujjar cewa Abba ya ajiye masu kujerar gwamna kafin ta fice daga jam'iyyar NNPP.
Kamfanin raba wuta na Kano watau KEDCO ya tabbatar da cewa an samu matsala a wata karamar tashar wuta bayan taransufoma ta kone, ya bai wa mutane hakuri.
A labarin nan, za a ji cewa wasu yara sun shiga farin ciki bayan an gano gawar mahaifinsu, nannade a cikin likkafani kamar yau aka birne shi bayan shekaru 20 a kasa.
Jihar Kano
Samu kari