Jihar Kano
Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga matasa da su yi taka tsantsan, kar su bari ayi amfani da su wajen rusa Kano da Arewa.
Rundunar 'yan sandan Katsina ta bayyana matsayarta na tabbatar da kakkabe 'yan daba daga cikin masu gudanar da zanga-zanga a jihar, inda aka kama yan daba 50.
Duk da yadda aka samu tashe-tashen hankula a wasu jihohin kasar nan saboda zanga-zanga, jama'a sun fara taruwa a Legas domin fara tattakin matsin rayuwa.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da ta sanya a fadin jihar a jiya Alhamis domin ba al'umma damar zuwa masallacin Juma'a.
Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar da hotuna da kuma bidiyo na yadda masu zanga-zanga ke satar dukiyar jama'a a Kano a ranar Alhamis.
Rundunar Kano sun bayyana nasarar cafke karin matasan da ake zargi da fasa wuraren ajiyar kayan abincin jama'a tare da wasosonsu a ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnoni hudu sun sanya dokar hana fita ta awanni 24 a jihohinsu yayin da zanga zangar lumana ta rikide zuwa tashin hankali.
An tafka ta'asa yayin gudanar da zanga-zanga ta ranar farko a birnin Kano da kewaye inda jama'ar gari da 'yan daba su ka rika satar kayan jama'a.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar mai martana Sarki Muhammadu Sanusi II. An ce sarkin ya cika shekara 63.
Jihar Kano
Samu kari