Kungiyar Shi'a
Manyan malamai da dama a Najeriya daga kowane bangare sun nuna alhini game da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi inda suka bayyana gudunmawarsa ga Musulmi.
Shugaban kungiyar IMN ta 'yan Shia'a a Najeriya, Ibrahim Zakzaky ya yi Allah wadai da maganar Trump kai kai hari Najeriya kan kashe Kiristoci a wasu jihohin kasar.
Kasar Iran ta yi magana kan ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi mata inda ta ce yaki da Isra’ila ya jawo mummunar barna a cibiyoyin nukiliya na kasar.
Jagoran addinin Musulunci ta Iran, Ayatullah Ali Khamenei ya yi magana bayan shafe kwana fiye da 10 ana yaƙi da Isra'ila inda ya bugi kirji kan nasararsu.
Duk da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila a jiya Talata, jagoran addini a kasar, Ayatullah Ali Khamenei bai ce komai ba.
Jami'an rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun cafke wasu wadanda ake zargi da hannu a arangamar da ta auku tsakanin 'yan shi'a da jami'an tsaro.
Kungiyar 'yan shi'a ta kasa (IMN) ta zargi jami'an tsaron Najeriya da shiga hakkinta ta hanyar hana membobinta gudanar da taro cikin lumana, bayan doka ta basu dama.
Rundunar 'yan sandan Abuja ta bayyana yadda zanga zangar 'yan Shi'a da rikice rikicensu da sauransu da suka jawo mutuwar 'yan sanda 140 a shekarar 2024.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daruruwan 'yan shi'a ne suka fantsama titunan Abuja domin nuna rashin jin dadi kan cin zarafinsu wadanda mafi yawansu mata ne.
Kungiyar Shi'a
Samu kari