Ibadan
Wasu fusatattun 'yan Najeriya da MTN ya rufewa layin waya a ranar Lahadi sun yiwa ofishin kamfanin tsinke a safiyar Litinin domin jin ba'asin abin da ya jawo hakan.
Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 19 kan zarginsa da ɓalle Masallaci tare da sace wayar zamani ta N100,000 ta wata mata.
An shiga jimami bayan mutuwar fitaccen basarake da ake kira Osi Balogun na Ibadanland, Oba Lateef Gbadamosi Adebimpe a jihar Oyo a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024.
Gwamnatin jihar Oyo ta ce dokar da Majalisa ta tabbatar wanda Gwamna Seyi Makinde ya sanyawa hannu ba ta da alaka da hana gadon kujerar Olubadan a jihar.
Rahotanni daga birnin Ibadan da ke jihar Oyo sun nuna cewa sabon Olubadan na ƙasar Ibadan, Oba Olakulehin ya kafa tarihi bayan naɗa masa rawanin sarauta yau Jumu'a.
An wayi gari da kulle gidajen mai a birnin Ibadan na jihar Oyo inda hakan ya jefa al'umma cikin matsala. Ma'aikata sun koka kan yadda lamarin ya kawo musu cikas.
Kwanaki bayan amincewa da bukatar masu nadin sarki, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sanya ranar 12 ga watan Yuli domin nadin sarautar sabon sarkin Ibadan.
Malamin Musulunci, Sheikh Muhydeen Bello ya soki 'yan siyasar Najeriya kan amfani da lokacinsu wurin taimakon al'umma inda ya bukaci su hada kai domin kawo ci gaba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi wasu ƴan gyare-gyare domin inganta ayyukan mambobin majalisar zartarwa, ta ɗauke wasu kwamishinoni ya canza masu wuri.
Ibadan
Samu kari