An Kama Dan Shekara 55 Da Ya Lalaba Cikin Dare Ya Saci Plantain Na N4,000 Daga Gonar Wani A Ibadan

An Kama Dan Shekara 55 Da Ya Lalaba Cikin Dare Ya Saci Plantain Na N4,000 Daga Gonar Wani A Ibadan

  • Sule Mosudi, wani mutum dan shekara 55 ya gurfana gaban kotu kan zargin satar Plantain ta N4000
  • Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargin ne misalin karfe na na dare yayin da ya kutsa gonar wani ya saci Plantain din
  • Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa da aikatawa kuma kotu ta bada belinsa kan kudi N50,000

Oyo - An gurfanar da wani mutun dan shekara 55, Sule Mosudi, a gaban alkalin kotun majistare na Iyaganku, Ibadan, kan zargin satar 'Plantain' da kudinsu ya kai N4000 daga gona, rahoton Premium Times.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa an gurfanar da Mr Mosudi na unguwar Abanla, Idi-Ayunre, Ibadan a kotun kan zarginsa da aikata sata.

Kara karanta wannan

Dan Sarki A Najeriya Ya Gayyaci 'Ƴan Kungiyar Asiri' Su Kashe Mahaifinsa Saboda Wata Sabani

Gudumar Kotu.
An Gurfanar Da Dan Shekara 55 Kan Satar Plantain Na N4,000 Daga Gonar Wani A Ibadan. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Lauyan mai shigar da kara, Foluke Oladosu ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Satumba misalin karfe 1 na dare a Abanla, Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Oladosu ta shaidawa kotu cewa an sato sinkin Plantain din ne dafa gonar wani Sikiru Oseni daga gonarsa da ke Iyana Ikija, Abanla, Ibadan.

Ta ce an kama wanda ake zargin ne saboda yan unguwar sun saka dokar hana kowa fita waje bayan karfe 11 na dare.

Oladosu ta ce laifin ya ci karo da tanadin sashi na 383 da 390 (9) na dokokin Criminal Code na Jihar Oyo ta shekarar 2000.

Martanin wanda ake tuhuma

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin.

Lauyan wanda ake zargin, Bode Akinbi, ya bukaci kotun ta bada belinsa.

Alkalin kotun, I.O. Soho, ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N50,000 da mutum biyu tsayayyu da za su karbe shi.

Kara karanta wannan

Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Ruwa A Jallo, Ta Bayyana Dalili

Mrs Soho ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba.

Alkali Ya Tura Dan Sufetan Yan Sanda Gidan Yari Kan Satar Motar N52m A Legas

A wani labarin, Alkalin kotun majistare da ke zamanta a Yaba a Legas ya bada umurnin a tsare wani Damilola Areje, a gidan yari kan satar mota, har sai ya cika ka'idojin beli.

Damilola, wanda iyayensa yan sanda ne, an bada belinsa kan kudi Naira miliyan 3 da mutane biyu wadanda ke da takardan biyan haraji na akalla shekara biyu da kuma a kalla gida daya a unguwan da kotun ke da iko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel