Matata Tana Azabtar Da Ni a Wurin Saduwa, Wani Magidanci Ya Nemi Kotu Ta Raba Su

Matata Tana Azabtar Da Ni a Wurin Saduwa, Wani Magidanci Ya Nemi Kotu Ta Raba Su

  • Wani magidanci ya garzaya Kotun Kostumare a Ibadan yana rokon a raba auren shi sabida matar na azabtar da shi da yunwar kwanciyar sunnah
  • Matar mai suna Nafisat ta shaida wa Alƙalin cewa ta amince da bukatar mijin domin ita ma ta gaji yawan bukatarsa
  • Bayan sauraron koken kowane ɓangare Kotun ta ɗage zaman zuwa watan Satumba mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Wani Mutumi, Rasheed Afeez, ya maka matarsa a gaban Kotun Kostumare dake zama a Ibadan, babban birnin Oyo, yana mai rokon Alƙali ya raba auren su bisa azabar da take masa a fannin kwanciyar aure.

Daily Trust tace Afeez, malamin makarantar Firamare ya shaida wa Kotun cewa, "Baki ɗayan su Shi da matar, Nafisat, sun san matsalar dake tattare da nau'in halittarsu tun kafin su yi aure."

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ɗan El-Rufai Ya Ce ASUU 'Bata Da Amfani', An Masa Zafafan Martani

Matsalar raba aure a Kotu.
Matata Tana Azabtar Da Ni a Wurin Saduwa, Wani Magidanci Ya Nemi Kotu Ta Raba Su Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa amma duk ba haka ba tare da tsammani ba ta fara hana shi haƙƙinsa na aure ba tare da wasu kwararan dalilai ba.

A jawabinsa ga Kotu, Malam Afeez ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba na tunanin sai na ƙuntata wa kaina wajen amfani da kwaroron roba wajen saduwa da ita saboda matata ce. Haka kawai na gano Nafisat na amfani da tsarin ƙayyade iyali ba tare da izini na ba."
"Mafi muni kuma ta tsiri shigar mutanen banza da kuma sauraron wakoki wanda ya saɓa wa koyarwan addinin mu, a takaice ma yanzu Nafisa ta koma kwana a Otal."

Shin matar ta amsa tuhume-tuhumen mijinta?

Da take maida martani, Nafisat ta yi na'am da bukatar datse igiyoyin aurenta da ya shafe shekara Tara tare da Afeez bisa dalilin takura mata da batun saduwa.

Nafisat, maasaniya a fannin magunguna wato Pharmacist kuma mahaifiyar 'ya'ya biyu, ta shaida wa Kotu cewa:

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

"Mai shari'a, Afeez ya maida ni wata abun saduwa kawai, kullum batunsa bukatar mu yi kwanciyar aure ne ba tare da duba illar hakan gare mu ba. Bai damu da sha'awata ba, matsalarsa kawai ya biya bukatarsa."
"Idan na ƙi yarda sai ya tilasta ni na saduda ta kowace hanya. Bugu da ƙari ina tsoron haihuwa da yawa saboda muna ɗauke da Sikila, ɗaya daga cikin 'ya'yan mu na ɗauke da nau'in halitta SS."
"Ni da Mijina muna da AS kuma ba ya sauke nauyin siyo magunguna ga ɗan mu dake fama da Sikila."

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Alƙalin Kotun, mai shari'a Misis S. M. Akintayo, bayan sauraron kowane ɓangare, ta dage zaman zuwa ranar 12 ga watan Satumba.

A wani labarin kuma Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

Wata mai jego mai suna Nizi Rozay, ta samu kyautar dankareriyar mota kirar Range Rover 2023 daga mijinta a matsayin kyautar nakuda bayan haihuwar dansu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar DSS Ta Saki Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar 'Yan Ta'adda a Najeriya

Maijegon wacce ke da yara uku ta je shafinta na Twitter don wallafa hotunan dankareriyar motar, kuma tuni suka yadu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel