Gwamnoniim G5 Sun Dira Wurim Gangamin Kamfen Gwamna Makinde a Oyo

Gwamnoniim G5 Sun Dira Wurim Gangamin Kamfen Gwamna Makinde a Oyo

  • Gwamnonin dake marawa Wike baya a PDP da aka fi sani da G5 sun mamaye Ibadan don kaddamar da kamfen Makinde
  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo na daya daga cikin mambobin G-5 kuma bai halarci taron Atiku ba a jihar
  • A wurin wannan gangamin ne ake tsammanin tawagar Wike zata ayyana dan takarar shugaban kasan da zasu marawa baya

Oyo - Fusatattun gwamnonin jam'iyyar PDP wadan da ake wa lakabi da G5 sun isa babban dakin taro Mapo Hall da ke kwaryar birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnonin sun isa wurin ne domin kaddamar da yakin neman tazarcen daya daga cikinsu, gwamna Seyi Makinde na jihar.

Wurin kamfe a Oyo.
Gwamnoniim G5 Sun Dira Wurim Gangamin Kamfen Gwamna Makinde a Oyo Hoto: Marshal Obuzor/facebook
Asali: Facebook

Sauran gwamnonin da suka haɗa tawagar gaskiya watau G-5 karƙashin jagorancin Nyesom Wike na jihar Ribas sune, Okezie Ikpeazu na Abiya, Samuel Ortom na Benuwai da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan Kano, Tinubu ya dura wata jiha domin tallata aniyarsa ta gaje Buhari

Rahotanni sun nuna cewa tawagar gwamnonin sun isa wurin da aka shirya kaddamar da kamfen da misalin karfe 1:00 na rana, yau Alhamis, 5 ga watan Janairu, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A halin yanzun an ce cunkoso na ababen hawa ya mamaye manyan Titunan da zasu kai ka zuwa Mapo Hall yayin da dubbannin magoya baya daga kananan hukumomi 33 na Oyo ke tururuwar zuwa taron.

Haka zalika, jami'an tsaron da aka girke domin ba da tsaro na iya bakin kokarin su wajen saita dandazon mahalartar kamfen don tabbatar da komai ya tafi a kan doka.

Sauran kusoshin PDP da suka halarci wurin

Tsofaffin gwamnoni kamar irinsu Olusegun Mimiko na jihar Ondo da Ayodele Fayose, sun hallara a wurin cikin shiga iri ɗaya da ta su gwamnonin G5, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

Tun da farko uwar gidan gwamna Makinde, Misis Tamunominini, ta isa dakin taron tare da rakiyar tsohuwar shugabar majalisar dokokin Oyo, Sanata Monsurat Sunmonu.

Mataimakin gwamna, Bayo Lawal, na wurin. Haka nan fitaccen mawakin Yarbawan nan, Saheed Osupa na kan dandamali lokacin da su Wike suka kunno kai.

A wani labarin kuma Shugaban PDP na kasa ya musanta rahoton da ake yadawa cewa ya lallaba Patakwal ya gana da Wike

Shugaban PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, yace kafarsa ba ta sauka a Patakwal ba balle idonsa ya yi tozali da gwamna Wike na Ribas.

Ayu ya karyata rahoton da ake yadawa cewa ya lallaba wurin Wike, yace Hoton da ake jingina wa labarin tsoho ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel