G5 a Dunkule Take, Zamu Sanar da Dan Takarar Mu Na Shugaban Kasa, Wike da Ortom

G5 a Dunkule Take, Zamu Sanar da Dan Takarar Mu Na Shugaban Kasa, Wike da Ortom

  • Gwamna Wike da takwaransa Samuel Ortom sun kawo karshen rade-radin da ake cewa an samu rabuwar kai tsakanin gwamnonin G5
  • Gwamnonin biyu sun ce kansu a hade yake kuma da zaran lokaci ya yi zasu fada 'yan Najeriya inda suka dosa a matakin kasa
  • A ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, gwamnonin suka jagoranci kaddamar da kamfen neman tazarcen Makinde a Ibadan

Ibadan, Oyo - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom, sun ce babu wata rabuwar kai a tawagar gaskiya watau G5 da ta balle daga PDP, har yau kansu a haɗe yake.

Gwamnonin biyu sun bayyana cewa nan ba da jimawa ba G5 zata sanar da dan takarar shugaban kasan da zasu marawa baya a zabe mai zuwa a watan Fabrairu, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamna Wike Ya Aike Da Sabon Muhimmin Sako Ga APC da Wasu Jam'iyyu

Kamfen gwamna Makinde.
G5 a Dunkule Take, Zamu Sanar da Dan Takarar Mu Na Shugaban Kasa, Wike da Ortom Hoto: Oyo News
Asali: Facebook

Wike da Ortom sun faɗi haka ne a dakin taron Mapo Halla dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo yayin kaddamar da kamfen neman tazarcen gwamna Seyi Makinde.

Cikin shigar al'ada da aka san Yarbawa da yinta, mambobin G5 da suka hada da Wike, Ortom, Ugwuanyi na Enugu da Ikpeazu na Abiya sun ja hankalin dumbin magoya bayan PDP su zabi Makinde karo na biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun ayyana takwaran na su da, "Shugaban matasan tawagar G5," wanda ke kokarin sake komawa matsayin gwamna a zango na biyu a zaben 2023.

Gwamna Wike ya roki mahalarta taron su zabi 'yan takarar PDP tun daga zaben gwamna, Sanatoci, majalisar wakilan tarayya da majalisar jiha.

"Ragowar ɗayan kuma (shugaban kasa) Seyi zai dawo ya fada masu," inji Wike yayin da yake tsokaci kna takarar shugaban kasan da G5 zata marawa baya, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

An ramawa Atiku: Gwamna mai ci da 'yan takarar gwamna 2 sun ki halartar kamfen PDP

Shin Ortom ya yi amai ya lashe kenan kan Obi?

Idan baku manta ba a wata sanarwa da kakakin Ortom, Terver Akase, ya fitar ranar Talata, gwamnan ya nuna goyon baya kan matakin Obasanjo na daukar Peter Obi.

Amma a ranar Alhamis a Ibadan, Ortom ya yi fatali da abinda ya kira, "Tsegumin Soshiyal midiya" inda ya bayyana cewa G5 zata sanar da 'yan Najeriya inda ta karkata a lokacin da ya dace.

"Muna tabbatar muku cewa gwamnonin G5 a shirye muke mu yi wa PDP aiki a jihohin mu. Muna da matsala da jam'iyya ta ƙasa saboda sun gaza warware damuwar mu."
"Mun sadaukar da kawunan mu ga PDP a jihohinmu kuma a lokacin da ya dace zamu fada maku abinda zaku yi. A dunkule muke, murya daya gare mu. Bamu sauraron gulmar soshiyal midiya."

- Samuel Ortom.

Shin Dagaske Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Wike?

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Gwamnonin G5 Sun Dira Wata Jihar da PDP Ke Mulki

A wani labarin kuma Ayu, wanda G5 ke neman ya yi murabus daga kujerar shugaban PDP ya musanta ganawa da Wike

Shugaban PDP na kasa ta bakin mai magana da yawunsa yace Hoton da ake jingina wa labarin ba yanzu aka dauke shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel