Tsaleliyar Budurwa Mai Tuka Tirela Ta Yada Bidiyo, Ta Jawo Cece-Kuce a Shafin Intanet

Tsaleliyar Budurwa Mai Tuka Tirela Ta Yada Bidiyo, Ta Jawo Cece-Kuce a Shafin Intanet

  • Wata mata 'yar Najeriya mai suna Omolade ta yada bidiyon sana'ar da take na tuka tirela, ta ce tana alfahari da hakan
  • Ma'aikatan da ke taya ta tukin mota na matukar alfahari da irin jajircewarta, kuma suna aiki cikin dadin rai
  • 'Yan Najeriyan da suka ga bidiyon a intanet sun sha mamaki, sun yi martani game da wannan bakon aiki a hannun mata

Wani bidiyo ya nuna wata 'yar Najeriya da ke tuka tirela, lamarin da ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

A shafinta na TikTok, matar ta yada bidiyo masu yawa na yadda take murza babbar mota kamar dai yadda maza ke yi. A daya daga ciki, an ga lokacin da take binciken kwa-kwaf ga motar kafin tashi.

Yayin da take kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yaran motarta sun dauki wani bidiyonta, sun bayyana yabo da kambata uwar dakin nasu.

Kara karanta wannan

Wasu Na Kishi: Matashi Ya Jinjinawa Matarsa Yayin da Take Girki Da Icce A Bidiyo

Matar da ke tuka tirela ta jawo cece-kuce a TikTok
Tsaleliyar Budurwa Mai Tuka Tirela Ta Yada Bidiyo, Ta Jawo Cece-Kuce a Shafin Intanet | Hoto: TikTok/@taiwoomolade1
Asali: UGC

Irin kwarewar da matar ta yi a tuki ya ba da mamaki, yayin da aka ga tana sarrafa motar daidai da yadda ake bukata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin da ke daukarta bidiyon sai yabonta yake, yana mai cewa waye ake dashi kwararren diraba kamar Omolade.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Ga kadan daga abin da jama'a ke tofawa bayan ganin bidiyon:

Sunday Okpe895 yace:

"Abu ya yi kyau 'yan mata, Allah ya ci gaba da kare ki."

Patricia Porteus tace:

"Nuna musu abin da mace za ta iya yi, Allah ya albarkace ya kare hanya."

putukeni 7 yace:

"Mace mai kamar maza, wannan ba kamarin aiki bane ki ci gaba da kokari kuma Allah ya tsare, Allah a tare dake a koyaushe...daga kasar Namibia."

Ace yace:

Kara karanta wannan

'Yar kirki: Bidiyon tsaleliyar budurwar da ke taya mahaifiyarta soya garin rogo ya jawo cece-kuce

"Ban taba ganin irin wannan abun ba a baya."

muyamajoy tace:

"Na dauki lokaci ina kallon bidiyon daga farko har karshe, kin burge 'yar uwa Allah ya ci gaba da yi miki albarka ya kuma kare ki. Abin da maza za su iya mu ma za mu iya."

'Yar TikTok Ta Sauke Jiji da Kai, Ta Nuna Sana’ar da Mahaifiyarta Ke Yi, Tana Taya Ta Aiki

A wani labarin, 'yan TikTok sun yiwa wata 'yar Najeriya mai kaudi a intanet tofin albarka saboda yadda take taimakawa mahaifiyarta.

A wani bidiyo da ta yada a asusunta na TikTok mai suna @brownsugarnice, ta shawarci 'yan mata masu kwalisa su ke taimakawa iyayensu.

Kasancewarta 'Slay Queen', hakan bai hana ta ayyukan gida, kuma takan yi amfani da lokacinta yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel