Labaran kasashen waje
Sabon shugaban rundunar yan sandan Najeriya, IGP Tunji Disu ya bayyana cewa rundunar na bibiyar abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya domin shirin ko ta kwana.
Adadin wadanda suka mutu a yaƙin Iran ya zarce 1,000 ciki har da yara 175. Amurka ta rasa sojoji 6, yayin da rikicin ya bazu zuwa Lebanon, Kuwait, da Iraki.
Naim Qassem ya ce Hezbollah ba za ta miƙa wuya ba yayin da Isra'ila ta kashe mutane 72 a Lebanon. Hezbollah ta farmaki sansanonin Haifa da Tel Aviv yau.
Amurka ta nutsar da jirgin yaƙin Iran yayin da Trump ya soki Biritaniya kan kin ba shi goyon baya ya kai hari Iran daga sansanoninta. Bayani kan yakin a rana ta 5.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta yi ikirarin cewa dakarun kasar sun yi ajalin wanda ke jagorantar rundunar da ke kitsa yadda za a ga bayan shugaban kasa, Donald Trump.
Makaman Iran sun daki Tel Aviv bayan sun ratsa ta babbar garkuwar tsaron Isra'ila, watau Iron Dome. An kashe mace 1 yayin da Amurka ta farmaki Tehran da Qom.
Iran ta ce ba za ta yi zaman sulhu da Amurka ba yayin da yaki tsakaninsu ya shiga rana ta biyar. Isra'ila ta ce Iran na da karfin makaman linzami har yanzu.
Sojojin juyin juya halin Musulunci na Iran sun tabbatar da harba makamai masu linzami guda 40 kan Amurka da Isra'ila. Amurka ta ruguza hedkwatar IRGC.
Iran ta kai hari Dubai da jirgi marar matuki a yau 3 ga Maris, 2026. Bidiyo ya nuna ofishin jakadancin Amurka yana ci da wuta daga nesa. An fara kwashe mutane.
Labaran kasashen waje
Samu kari