Yadda aka Tura wa Gwamnoni 36 Zunzurutun Kudi Sama da Naira Tiriliyan 4
- Jihohi 36 na ƙasar nan sun sami tsabar kuɗi har Naira triliyan 4.83 daga asusun FAAC tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2026
- Binciken ya nuna cewa jihohin Delta, Lagos, Rivers, Akwa Ibom da Bayelsa ne suka fi kowace jiha samun mafi yawan kuɗin
- Jihar Delta ce ke kan gaba da naira biliyan 369.87, yayin da jihar Cross River ta kasance ta ƙarshe da naira biliyan 75.87
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jihohi 36 na Najeriya sun samu jimillar kuɗi har naira triliyan 4.83 daga asusun FAAC tsakanin watan Janairu da Yunin shekarar 2026.
Binciken da aka gudanar kan kuɗin da aka raba wa jihohin a cikin wata shida ya nuna cewa jihohin Delta, Lagos, Rivers, Akwa Ibom da Bayelsa ne suka samu mafi yawan kason kuɗin.

Kara karanta wannan
Kakar miliyoyin matasa ta yanke saƙa, an fadada shirin tallafin rage talauci a Najeriya

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa waɗannan kuɗi ana tsammanin za su taimaka wa jihohin wajen sauke nauyin da ke kansu na tsarin mulki, da suka haɗa da biyan albashin ma'aikata da haƙƙoƙinsu da sauransu.
Jihohin da suka fi samun kason
Jihar Delta ce ta amshi mafi yawan kason FAAC inda ta samu naira biliyan 369.87, sai jihar Lagos ta biyu da naira biliyan 368.79, Rivers ta samu biliyan 331.73, Akwa Ibom ta biyo baya da biliyan 300.73, yayin da Bayelsa ta samu biliyan 289.19.
Jihar Kano ce ta kasance a matsayi na farko a tsakanin jihohin da ba sa fitar da man fetur inda ta samu naira biliyan 158.49.
Baya ga jihohin da ke samar da man fetur, sauran jihohin da suka sami babban kaso sun haɗa da Oyo da aka bawa biliyan 147.32, Ondo biliyan 119.44, Borno biliyan 116.13, yayin da Imo ta samu biliyan 115.19.
Jihohi masu karancin kason FAAC
Bayanai sun nuna cewa akwai jihohi 10 da suka sami mafi ƙancin kaso na FAAC. Misali, Nasarawa ta samu naira biliyan 92.87, Kaduna biliyan 92.28, Kwara biliyan 90.10, Bauchi biliyan 89.79, sai Ebonyi da ta samu biliyan 89.06.
Haka zalika, Osun ta samu biliyan 87.64, Ogun biliyan 83.27, Gombe biliyan 82.61, Ekiti biliyan 80.54, yayin da jihar Cross River ta sami mafi ƙancin kaso a cikin jihohi 36 inda ta samu naira biliyan 75.87.

Source: Facebook
A cewar rahoton:
"A kowane wata, kuɗin shiga da gwamnatin tarayya ta tara daga haraji, man fetur, da sauran hanyoyi ana zuba su ne a asusun tarayya, inda kwamitin FAAC ke gudanar da taro a kowane wata domin raba su daidai da tanadin tsarin mulki."
Gwamnatin tarayya tana amfani da 52.68% na kuɗin, jihohi 26.72%, ƙananan hukumomi 20.60%, yayin da jihohi masu arzikin fetur ke samun ƙarin 13% na kason albarkatun fetur.
NLC ta nemi rage kudin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako biyu domin rage farashin man fetur.
Wa'adin ya fara aiki ne daga ranar Juma'a, inda babbar ƙungiyar ma'aikatan ta faɗaɗa gargaɗin cewa idan har gwamnati ta ƙasa cika buƙatun nata za ta dauki mataki,
Sanarwar wadda Shugaban NLC, Joe Ajaero ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, ta bayyana damuwa matuka kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta.
Asali: Legit.ng

