Labaran kasashen waje
Firayim Ministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya goyi bayan yunƙurin Pakistan na shiga tsakanin Amurka da Iran domin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Firaministan kasar Spain, Pedro Sanchez, ya ragargaji Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Ya bayyana cewa yana da mugun nufi kan kasar Lebanon.
Iran na ci gaba da harba makamai masu linzami kan Isra'ila yayin da ake ci gaba da fafatawa a Gabas ta Tsakiya. Makaman na Iran sun yi barna a wasu birane.
Harin makami mai linzami da Iran ta kai Tel Aviv a ranar 24 ga Maris ya kashe aƙalla mutane 16, tare da ruguza gine-gine da jikkata wasu da dama.
Tarayyar Turai (EU) da Najeriya sun amince su faɗaɗa haɗin gwiwa kan hakar ma'adanai, tsaro, da kasuwanci yayin da ake fama da yaki a Gabas ta Tsakiya.
Yarima Mohammed bin Salman ya matsa wa Donald Trump lamba domin ya ci gaba da yaƙi da Iran, inda ya bayyana lamarin a matsayin "dama" ga yankin Gabas ta Tsakiya.
Harin makami mai linzami daga Iran ya lalata wasu manyan gine-gine a birnin Tel Aviv na Isra'ila, inda mutane huɗu suka sami raunuka a ranar Talata.
Binciken sojin Isra'ila ya tabbatar da cewa kuskuren lissafi ne ya sa dakarun ƙasar suka harba makaman atilare kan wani manomi maimakon mayakan Hezbollah.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya fara tattauna da kasar Iran don samun mafita a yakin da ake yi. Iran ta yi martani kan wannan ikirarin.
Labaran kasashen waje
Samu kari