Yaki da ta'addanci a Najeriya
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bukaci a yi watsi da sulhu da Bello Turji ya ce zai yi da gwamnati. Ya bukaci a kashe dan ta'addan.
Rundunar yan sandan Kano ta gurfanar da wadanda ake zargi da tayar da zaune taaye a zaben cike gurbim da aka gudanar a mazabun yan majalisa 2 ranar Asabar.
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da kai hari masallacin kauyen Unguwan Mantau da ke yankin karamar hukumar Malumfashi a Katsina, an kashe mutane 13.
Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun yaba wa Najeriya da malam Nuhu Ribadu kan kama shugabannin 'yan ta'addan Mahmuda a Najeriya a makon da ya wuce.
An gano bam a gonar manomi a Dikwa, Borno, inda jami’an ’yan sanda suka kwance shi cikin nasara tare da wayar da kan jama’a game da illolin abubuwan fashewa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama kudi Naira miliyan 6.9 da bindigogi bayan 'yan bindiga da suka karbo kudin fansa suna kokarin guduwa a jihar Nasarawa.
Fadar shugaban kasa ta ware mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu inda ta jero abubuwan alheri da ya yi cikin wata 25 da ya yi a ofishinsa.
Yaran dan ta'adda, Bello Turji sun kai hare hare jihar Sokoto. Sun kashe mutane da dama tare da sace wasu. Sojoji sujn ce har yanzu suna neman Turji ido rufe.
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kama manyan shugabannin kungiyar Ansaru da suka jagoranci harin gidan yarin Kuje.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari