Gwamnatin tarayyar Najeriya
Gwamnati ta shekara tana yaudara, dangi sun gaji sun rufe mutumin da ya kirkiro tutar Najeriya. Taiwo Akinkunmi ya rasu ya na shekara 87 a watan Satumban bara.
Ana tuhumar CBN da batar da biliyoyin kudi domin sayen motoci da sunan kama hayan gidajen haya. An yi sama da kusan N10bn domin motocin gwamna da mataimakansa.
Rahoto ya bayyana cewa kimanin mutane 13,346 aka kashe yayin da aka sace wasu 9,207 daga hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki zuwa watan Satumbar 2024.
Gwamnatin tarayya ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ta kayyade shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin zama jarabawar WAEC da NECO, ta ce ba gaskiya ba ne.
Hukumar kula da ayyuka kasuwanci a Najeriya CAC ta ce za ta sa ƙafar wando ɗaya da duk mai sana'ar POS da ya gaza yin rijista kafin cikar wa'adin da ta ɗiba.
Gwamnatin tarayya ta ce ambaliyar ruwa za ta iya yiwa wasu jihohi 21 illa a nan gaba kadan. Gwamnatin ta bayyana sunayen jihohi 7 da ambaliyar za ta fi yiwa barna.
Daga watan Yulin 2023 zuwa watan Yunin 2024, Najeriya ta zama kasa ta 3 a jerin ƙasashen da ke sahun gaba a yawan cin bashin bankim dumiya na IDA.
'Yan majalisa marasa rinjaye na majalisar wakilai sun yi Allah wadai da karin kudin man fetur da aka yi. Sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta cire karin.
Shugaban TUC, Festus Osifo ya bukaci gwamnatin tarayya ta soke ƙarin da ta yi a farashin litar man fetur, ta ce duk wannan wahalhalun a kan ma'aikata za su ƙare.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari