Gwamnatin tarayyar Najeriya
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Ministan Kudi Wale Edun ba ya cikin hadari, bayan rahoton rashin lafiyarsa da jita-jitar cewa za a maye gurbinsa.
Minista Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ce auren wuri yana hana ci gaban Najeriya, inda 44% na ‘yan mata ke yin aure kafin shekara 18, bisa bayanan hukumar UNICEF.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da yi wa mutane 175 afuwa cikinsu har da wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, Maryam Sanda za ta koma cikin iyalanta.
Ministan ma'adanai, Dele Alake ya nunka tsaronsa bayan samun barazanar kisa daga wadanda aka soke wa lasisin hakar ma’adinai, duk da umarnin Shugaba Tinubu.
Kungiyoyin Ma'aikatan Jami'o'i da Kwalejojin Ilimi na Tarayya aun fara zanga zangar lumana kan rashin cika alakwarin gwamnatin Najeriya tun 2009.
Tsohon gwamna kuma Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya karyata ikirarin Olusegun Obasanjo cewa labarin da ake yadawa cewa ya nemi zango na uku ba gaskiya ba ne.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta saki jagoran kungiyar yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.
Taraba, Kogi da wasu jihohin Arewa za su samu ruwan sama a yau Alhamis yayin da ake bankwana da damina. An gargadi mutane su shirya wa ambaliya a yankunansu.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen kisan da ake yi wa Kiristoci. Ta bukaci a ba su kariyar da ta dace.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari