Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ruwan da ke shiga madatsar Alau ne ya fi karfinta, wanda ya sa ta fara neman hanyar fita zuwa cikin gari ta sama.
Gwamnatin tarayya, ta bakin hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas ta bayyana cewa rashin kargon gini da cushewar ruwa a madatsar Alau ya jawo ambaliya a Maiduguri.
Kungiyar yan Arewa ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kaucewa bin hanyar Muhammadu Buhari. Kungiyar ta ce Buhari ne ya jefa Tinubu a matsala.
Kungiyar kwadago ta bayyana cewa za ta kai shugabanta, Joe Ajaero asibiti domin tabbatar da lafiyarsa bayan kamun da DSS ta masa. NLC ta bukaci a saki takardunsa.
Primate Elijah Babatunde Ayodele ya fitar da wani sabon hasashe a game da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar NEMA ta gaggauta kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Maiduduri, yana mai jajantawa gwamnatin Borno.
Ambaliyar ruwa ta rusa gidan dabbobi da ke Maiduguri a jihar Borno. Dabbobi kamar kada da macizai sun shiga gari ta cikin ruwa. Kashi 80 na dabbobi sun mutu.
Jam'iyyar APC mai mulki ta barranta da maganar takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa. An hango alluna takarar shugaban kasar a Abuja
Tsohon mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Dakta Reuben Abati ya ce yanzu haka tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na can yana yiwa Najeriya dariya.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari