Gwamnatin Najeriya
Kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya ta bayyana cewa ofishin NSA zai taimakawa gwamnoni wajen kara inganta tsaro yayin da ake shirin yin zanga zanga.
Hukumar kula da tashoshin ruwa ta kasa (NPA) ta bayyana cewa ta yi nasarar tattarawa gwamnatin tarayya makudan kudin shiga a cikin shekara uku da ya kai N1.423trn.
Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci kamfanin rarrabe wutar lantarki da NERC da su koma tsohon farashin kudin wutar lantarki na kwastomomin Band A, a cire ƙarin.
Gwamnatin tarayya ta kara daukan sabon mataki bayan shugaba Bola tinubu ya ba matasa hakuri kan zanga zanga a jiya Talata. A yau Laraba ne za su zauna a Abuja.
Kungiyar matasa a Kano ta bayyana cewa ta na kan matsayarta na shiga zanga-zanga matukar gwamnatin tarayya ta ba dauki matakin kawo sauki ga talaka ba.
Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya samu gayyata daga shugaban kasar Gabon, Brice Oligui Nguema domin ya zuba jari a harkar siminti da taki.
Shugaban bankin Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina ya ce fadi-in-fada da ke wakana tsakanin attajirin nahiyar nan, Aliko Dangote da gwamnatin tarayya babbar illa ce.
Shahararren marubuci, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa ba zai ce komai a kan salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba duk da ya yi alkawarin haka.
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Accra na kasar Ghana, bayan halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 6 na kungiyar Tarayyar Afirka.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari