Yan bindiga
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun sake kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Ihima a Kogi inda yan sanda sun cafke mutum ɗaya.
Mai martaba Tor Tiv, James Ayatse ya yi bayanai a gaban Shugaba Bola Tinubu kan halin da ake ciki a Benue. Ya ce suna fuskantar kisan kare dangi daga 'yan ta'adda.
Majalisar Benue ta zargi jami'an tsaro da kin tabuka abin kirki yayin da 'yan bindiga ke yi wa jama'a kisan gilla. Majalisa ta bukaci mazauna jihar su kare kansu.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun hallaka mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu zuwa daji.
Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a majalisar dattawan Najeriya, Seriake Dickson, ya bayyana gibin shugabanci a matakin kananan hukumomi na rura sashin tsaro.
Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen Marmara da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, sun halaka dakarun CWC guda hudu da manoma masu yawa.
Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum da ke saka kayan soji yana fashi da makami da satar mutane. Sun kai samame wata maboyar 'yan bindiga a Filato
Gwamnatin jihar ta aika da sakon gargadi ga tubabbun 'yan bindigan da suka ajiye makamansu. Ta ce za su fuskanci hukunci idan suka saba alkawari.
Benue na fuskantar hare-haren 'yan bindiga; sama da 100 sun mutu, dubbai sun rasa matsuguni. NEMA na neman agaji yayin da aka kafa sansanin 'yan gudun hijira.
Yan bindiga
Samu kari